Atiku bai taba samun nasarar zabe a kai na ba - Buhari

Atiku bai taba samun nasarar zabe a kai na ba - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ya yi bugun gaba na fifiko a siyasance ga babban abokin adawarsa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya misalta Atiku a matsayin dan siyasa da faduwar zabe ke bibiyar sa a duk inda ya sanya gaba. Ya ce faduwar zabe ga Atiku ta zamto tamkar jinin jikin sa.

Atiku bai taba samun nasarar zabe a kai na ba - Buhari

Atiku bai taba samun nasarar zabe a kai na ba - Buhari
Source: UGC

Yayin kalubalantar korafin Atiku na rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019, shugaban kasa Buhari cikin bugun gaba da nuna fifiko, ya ce Atiku bai taba cin galabar zabe a kansa ba.

Shugaban kasa Buhari ya hikaito yadda ya rika cin galaba a kan Atiku a duk wani zabe da su ka tsaya takara tare cikin jam'iyya daya ko kuma sabanin haka. Ya bayar da misalin yadda ya lallasa Atiku yayin zaben fidda gwanin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC a shekarar 2014.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta shigar da kudirin inshorar lafiya cikin dokar kasa

Buhari wanda ya lashe babban zaben bana na kujerar shugaban kasa a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, ya ce Atiku da jam'iyyar sa ta PDP ba su da hurumin neman kotun daukaka ta soke zaben sakamakon rashin kwararan dalilai da kuma hujjoji.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Atiku wanda ya kasance tsohon mataimakin shugaban kasa ya gabatarwa da kotun daukaka kara kwararan hujjoji da ke tabbatar da cewa shi ya yi nasara a zaben shugaban kasa na bana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel