Ba mu kulla yarejejeniyar cire tallafin man fetur da IMF ba - Ministar kudi

Ba mu kulla yarejejeniyar cire tallafin man fetur da IMF ba - Ministar kudi

Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta karyata rahotannin wasu kafafen yada labarai da ke cewar gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniyar cire tallafin man fetur da kungiyar lamunin kudi ta duniya (IMF).

Ministar ta bayyana hakan ne yayin da ta ke amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan fitowa daga taron majalisar zartar wa ta tarayya (FEC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ta ce gwamnatin tarayya za ta iya cire tallafin man fetur ne kawai idan ta gama samun matakan da zasu dauke radadin janyewar a kan 'yan kasa.

"A satin da ya gabata mun tattauna da manema labarai bayan taron da muka yi da IMF da Bankin Duniya

"Ba mu yi magana a kan tallafin man fetur ba. Wani dan jarida ne kawai ya yi tambaya a kan wani rahoton IMF da ya karanta.

Ba mu kulla yarejejeniyar cire tallafin man fetur da IMF ba - Ministar kudi

Ministar kudi; Zainab Ahmed
Source: UGC

"Ya tambayi ko mu na da shirin cire tallafin man fetur, ko mun cimma wata yarjejeniya da IMF a kan cire tallafin man fetur.

"To, bari na fada muku; babu wani wuri da IMF ta taba gudanar da bita ba tare da ta bayar da shawarwari ba, hakan ma shine dalilin yin bitar.

"Sun ba mu shawarar mu cire tallafin man fetur bayan sun yi bita a kan dalilin da ya sa mu ke biyan kudin tallafin man fetur, ba iya Najeriya suka bawa wannan shawara ba.

DUBA WANNAN: Kotu ta bawa EFCC damar kama wasu manyan ministoci biyu a gwamnatin PDP

"Amsar da na bawa mai tambayar shine mun amince da shawarar. Amma dole mu nemo hanyar da zamu aiwatar da shawarar da suka bayar. Ta ya ya za mu yi hakan?

"Za mu cire tallafin man fetur ne kawai idan mun samu abubuwan da zasu dauke radadin cire tallafin daga kan 'yan kasa.

"Alhakin bangaren zartar wa ne da masu yin doka su amince a kan wadanne abubuwa ne zasu dauke radadin daga kan 'yan kasa," a cewar Ministar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel