Yanzu-yanzu: Buhari zai sallami dukkan ministocinsa

Yanzu-yanzu: Buhari zai sallami dukkan ministocinsa

Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya tsaf domin sallamar dukkan ministocinsa yayinda wa'adinsa na farko zai kare a ranar 29 ga watan Mayu, 2019.

Buhari wanda ya samu nasara a zaben wa'adinsa na biyu a watan Febrairu ya saki jawabi jiya Talata inda ya umurci sukkan ministocinsa su sallama dunkulallen rahoton ma'aikatunsu kafin sallamarsu.

An basu zuwa ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu, su kai wannan rahoton sashe bincike na ofishin mataimakin shugaban kasa.

Kana an umurcesu su sallamar da dukkan takardun da basu kawo majalisar zantarwa ba zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya nan zuwa ranar Talata, 30 ga watan Afrilu, 2019.

Jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, yace:

"Yayinda wa'adin shugaba Muhammadu Buhari na farko ke karewa, shugaban kasan ya bukaci rahoton ayyuka daga ministoci da ma'aikatunsu."

"An baku zuwa ranar 24 ga watan Laraba, 2019 su sallamar da wannan rahoto kwamitin binciken ofishin mataimakin shugaban kasa."

Mun kawo muku a baya cewa, Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari zai sallami zai sallami ministocinsa kafin ranan 29 ga watan Mayu.

Bayan hawa mulki a shekarar 2015, sai da ya kwashe watanni shida kafin nada ministoci kuma hakan ya jawo masa cece-kuce.

Ya yi bayani a tashar Arise TV, Femi Adesina ya ce shugaban kasa ba zai dau lokaci irin haka kafin ya nada ministoci ba wannan karon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel