A dakatar da sintirin Operation Puff Adder a Ebonyi – Umahi ya roki IGP

A dakatar da sintirin Operation Puff Adder a Ebonyi – Umahi ya roki IGP

- Gwamnan Ebonyi ya roki IGP ya dakatar da shirin Operation Puff Adder

- David Umahi ya bayyana cewa an daina rikici a Yankin da fada ya barke

- Gwamnan Jihar yace an samu zaman lafiya a Garuruwan Ikwo da Abakaliki

Mun ji labari cewa Gwamnan Jihar Ebonyi, mai girma David Umahi yayi magana a game da shirin da dakarun ‘yan sandan Najeriya su ke yi na soma Operation Puff Adder, inda yace ya kamata Rundunar ta dakatar da wannan shirin tukuna.

David Umahi yake cewa zai zauna da jami’an ‘yan sanda da ke yankin da su cire damarar da su kayi na shirin Operation Puff Adder. Umahi yana nema a ba shi lokaci na tsawon mako guda domin yayi bincike kan rikicin da ya barke a jihar.

Gwamnan ya roki Sufeta Janar na ‘Yan Sandan kasar, Mohammed Adamu, da ya dakatar da shirin da Rundunarsa ke yi na kutsawa cikin Garuruwan jihar na Ebonyi. Gwamnan yayi wannan kira ne a jiya Ranar Talata 16 ga Watan Afrilu.

KU KARANTA: Takaddama da Shugaban Majalisa ya jawo an kori Honarabul

A dakatar da sintirin Operation Puff Adder a Ebonyi – Umahi ya roki IGP

Gwamna Umahi yace an samu tsaro a Jihar Ebonyi
Source: Depositphotos

Mai Girma Gwamnan yake cewa an samu zaman lafiya a bangarorin jihar da ake ta fama da rikici a da. Dave Umahi yace a halin yanzu babu wani tashin hankalin da ake fuskanta a cikin karamar hukumar Ikwo da kuma cikin Garin Abakaliki.

A jiyan ne dai wani babban jami’in ‘yan sandan kasar watau wani mataimakin sufeta janar mai wakiltar yankin Ebonyi da kewaye, AIG Musa Kimo, ya kai wa gwamnan ziyara. Kimo ya yabawa kokarin da gwamna yake yi na kawo zaman lafiya.

Umahi yake cewa ya zauna da mutanen yankin inda su ka cin ma matsayar za a samu zaman lafiya na din-din-din a yankin don haka yake ganin babu dalilin a aika Dakarun ‘yan sanda a cikin makon nan har sai idan abubuwa sun yi tsami.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel