Dalilin da ya sa aka daina jin duriyata – CP Wakili

Dalilin da ya sa aka daina jin duriyata – CP Wakili

- Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Wakili ya fayyace dalilin da yasa aka daina jin bakinsa

- CP Wakili yace yana nan yana ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata

- Yace ba a jin bakinsa saboda yanzu ba lokaci bane na zabe

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Wakili ya bayyana dalilin da yasa aka daiuna jin bakinsa kwana biyu.

Ya ce yana nan kan bakarsa kuma suna aikinsu yadda ya kamata ba dare ba rana.

An rahoto kwamishinan na cewa: "A baya ana ta jin duriyata saboda lokacin zabe ne.”

Dalilin da ya sa aka daina jin duriyata – CP Wakili

Dalilin da ya sa aka daina jin duriyata – CP Wakili
Source: UGC

"Idan ana kacaniyar neman zabe akwai abubuwa da dama wadanda na tsaro ne kuma yana dauke hankalin jama'a.

"Saboda haka yana bukatar a ji tabbacin cewa za a yi lafiya a kammala lafiya...wanda yake duk yanzu babu su.”

Daga nan ya ce yana nan lafiya lau kuma yana aikinsa yadda ya kamata.

KU KARANTA KUMA: Gudun abin kunya: Tsohon shugaban kasar Peru ya harbe kan sa

Da aka tambaye shi akan lamarin shaye-shaye a jihar Kano, CP Wakili ya ce tun da aka kammala zabe zuwa yanzu sun kama 'yan daba wadanda suke kurkuku fiye da 930.

Ya ce masu tu'ammali da miyagun kwayoyin sun suaya salo, "amma a yanzu haka muna binciken wani muhimmin batu."

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa, uwargidar Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, na ganawar sirri da matan gwamnonin jihad a wasu kwararru a fannin tsaro.

An kira taron ne a kokarin ba mata damar bayar da gudunmawarsu waje magance matsalar sace-sacen mutane, fashi da makami da sauran lamarin rashin tsaro a kasar, jaridar NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel