Aisha Buhari ta gana da matan gwamnoni da kwararru a harkar tsaro kan rashin tsaro

Aisha Buhari ta gana da matan gwamnoni da kwararru a harkar tsaro kan rashin tsaro

- A yanzu haka Uwargidar Shugaban kasa, Aisha Buhari na ganawa da matan gwamnoni da kwararru a fannin tsaro, domin bayar da gudunmawarsu a kokarin magance matsalar rashin tsaro a kasar

- Anyi ganawar ne domin karfafa goyon bayan lamarin magance matsalar tsaro ta fuskacin iyaye mata

- Ana zuba ido don jin sakamakon ganawar

Uwargidar Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, na ganawar sirri da matan gwamnonin jihad a wasu kwararru a fannin tsaro.

An kira taron ne a kokarin ba mata damar bayar da gudunmawarsu waje magance matsalar sace-sacen mutane, fashi da makami da sauran lamarin rashin tsaro a kasar, jaridar NAN ta ruwaito.

Aisha Buhari ta gana da matan gwamnoni da kwararru a harkar tsaro kan rashin tsaro

Aisha Buhari ta gana da matan gwamnoni da kwararru a harkar tsaro kan rashin tsaro
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa taron wwanda uwargidar Buhari ta kira, ya kasance don karfafa goyon bayan magance matsalolin rashin tsaro daga fuskacin iyaye mata.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya rufe wani babban Otel da ake aikata fasadi a jihar Kano

Musamman zai ta’allaka waje rage rikice-rikice da kuma tabbatar da bayar da agaji a wuraren da abun ya shafa.

Ana zuba ido don jin cikakken bayani da sakamakon ganawar a karshen taron.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa, Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Al-Makura ya baiwa jami’an tsaro kwana bakwai da su nemo wadanda suka aikata ta’addanci da ya auku a kauyen Numa Kochu da ke karamar hukumar Akwanga wanda yayi sanadiyar rayukan mutane 16.

Gwamnan ya bada wannan umurnin ne yayinda ya kai ziyara ga wadanda suka samu rauni sakamakon faruwa wannan abu wadanda ke jinya a babban asibitin Akwanga ranar Talata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel