Majalisar Dattawa ta shigar da kudirin inshorar lafiya cikin dokar kasa

Majalisar Dattawa ta shigar da kudirin inshorar lafiya cikin dokar kasa

Da sanadin jaridar The Punch mun samu cewa, majalisar dattawan Najeriya a ranar Laraba ta rattaba hannu tare da bayar da sahalewar ta wajen shigar da kudirin inshorar lafiya na shekarar 2019 cikin dokar kasa.

Shugaban Majalisar Dattawa; Abubakar Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa; Abubakar Bukola Saraki
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, majalisar ta shigar da wannan sabon kudiri cikin doka yayin zaman ta da ta gudanar a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu.

Majalisar ta shigar da kudirin inshorar lafiya cikin dokar kasa biyo bayan sakamakon bincike a kan kudirin da kwamitin majalisar mai kula da harkokin lafiya ya gudanar bisa jagorancin wakilin shiyyar Ogun ta Tsakiya, Sanata Lanre Tejuoso na jam'iyyar PDP.

Yayin jagorancin zaman majalisar da shugaban majalisar dattawa ya gudanar, Abubakar Bukola Saraki, ya buga sandar iko a kan sabon kudirin bayan an karance shi sau uku a zauren majalisa.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta bayar da hutu a ranar Juma'a da Litinin

Kazalika majalisar yayin zaman ta a ranar Laraba, ta shigar da sabon kudirin hukumar 'yan sanda mai lamba 683 cikin dokar kasa bayan kwamitin kula harkokin hukumar 'yan sanda ya gabatar da sakamakon binciken sa bisa jagorancin wakilin shiyyar Zamfara ta Arewa, Sanata Tijjani Kaura na jam'iyyar APC.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel