Gwamnatin tarayya ta bayar da hutu a ranar Juma'a da Litinin

Gwamnatin tarayya ta bayar da hutu a ranar Juma'a da Litinin

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da hutun aiki na kwanaki biyu a ranakun Juma'a, 19 ga wata da kuma ranar Litinin, 22 ga watan Afrilun 2019. Gwamnatin ta kaddamar da hutun domin bai wa mabiya addinin Kirista damar gudanar da bukukuwan Easter.

Babbar sakatariyar dindindin ta ma'aikatar harkokin cikin gida, Georgina Ehuriah, ita ce ta bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba a garin Abuja.

Abdurrahman Dambazau

Abdurrahman Dambazau
Source: Depositphotos

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Laftanar Janar Abdurrahman Danbazau, wanda ya kaddamar da hutun a madadin gwamnatin tarayya, ya nemi mabiya addinin Kirista da su yi koyi kyawawan dabi'u na soyayya da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Janar Dambazau ya yi kira na neman dukkanin al'ummar Najeriya na nan gida da kuma na waje, a kan su ribaci wannan lokaci wajen gudanar da addu'o'i na zaman lafiya da kuma hadin kai domin tabbatuwar ci gaban kasa.

KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya rufe wani babban Otel da ake aikata fasadi a jihar Kano

Ya kuma yi kira na neman al'ummar kasar nan wajen goyon bayan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da ta ke ci gaba da zage dantse da kuma daura damarar karkatar da akalar jagoranci a bisa akida ta matakin gaba wato Next Level.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel