Jami'an kwastam sun kama motar dakon kaya makare da katan 600 na kodin

Jami'an kwastam sun kama motar dakon kaya makare da katan 600 na kodin

Wata rundunar jami'an kwastam a shiyyar 'A' da ke Legas, ta kamawata babbar motar dakon kaya makare da kwayar sinadarin kodin da kudinta ya kai N240m.

Babbar motar mai lamba: LSR 944 XF na dauke da katan 600 na kodin, kuma an kama ta ne a 'Mile 2' da ke babban titin jihar Legas.

A cewar shugaban kwastam na shiyyar, Aliyu Mohammed, an shigo da kayan ne ta daya daga cikin iyakokin Najeriya da ke yankin, ya ce ba su san inda za a kai kwayar ba.

Mohammed ya kara da cewa direban motar ya gudu bayan ya hango tawagar jami'an kwastam yayin da suke gudanar da sintiri.

"Ba zamu taba daina kama miyagun kwayoyi ba. Dole mu kare yunkurin rusa kasar mu da wasu tsirarun mugaye ke kokarin yi.

Jami'an kwastam sun kama motar dakon kaya makare da katan 600 na kodin

Jami'an kwastam sun kama motar dakon kaya makare da katan 600 na kodin
Source: UGC

"Rundunar kwastam ba ta nuna kiyayya ga mutane. Mu na yin aikin mu ne na kare kasa da jama'ar ta. Jami'an mu a shirye suke su kama irin wadannan miyagun kayayyaki," a cewar Mohammed.

Mohammed ya kara da cewa a tsakanin watan Fabrairu zuwa Maris, shiyyar da ya ke jagoranta ta kama sacet 1,000 na turamol, buhun shinkafa 13,810 da kuma wasu kwayoyi da kudinsu ya kai N105,600,000 da sauran su.

DUBA WANNAN: Kotu ta bawa EFCC damar kama wasu manyan ministoci biyu a gwamnatin PDP

Daga cikin kayan da aka kwace akwai wata motar kamfanin Dangote da aka yi amfani da ita wajen shigo da buhun shinkafa 800 ta iyakar Najeriya.

"Mun kama har motar saboda ana amfani da ita wajen shigo da haramtattun kaya cikin Najeriya. Yanzu ta zama mallakar gwamnatin tarayya, kuma za a yi gwanjonta idan da bukatar hakan," a cewar Mohammed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel