Mutum takwas ne suka mutu, yayinda 148 suka samu rauni cikin watanni uku, inji Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC)

Mutum takwas ne suka mutu, yayinda 148 suka samu rauni cikin watanni uku, inji Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC)

-Hadurra arba'in da tara ne suka auku cikin watanni uku a jihar Filato

-Wasu mutanen sun rasa rayukansu, inda kuwa wasu suka samu mummunan rauni

Hukumar kare hadurra ta kasa shiyar jihar Filato ta bayyana mana cewa mutum takwas ne suka rasa rayukansu inda kuma mutum 148 suka samu rauni sakamakon hadurra 49 da suka auku a jihar, tsakanin watan Janairu da Maris.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Jos, jam’in hukumar mai kula da sashen ilimantar da jama’a, Andrew Bala yace, akasarin hadurran sun faru ne sanadiyar mugun gudu da masu abin hawa keyi a bisa titi. Inda ya kara da cewa wasu dalilan kuwa sun hada da matsalar burki da kuma sudewar taya.

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Harin Nasarawa: Al-Makura ya baiwa jami’an tsaro kwana bakwai su nemo masu laifin

“A watan Janairu mun samu hadurra goma sha uku inda babu wanda ya mutu, amma sai dai mutane talatin da biyu ne suka samu munanan raunuka. A watan Fabrairu, mun samu hadurra goma sha shida inda mutum uku suka rasa rayukansu sai kuma mutum talatin da biyu da suka samu rauni. A watan Maris, hadurra ashirin muka samu, mutum biyar ne suka mutu inda kuma mutane tamanin da hudu suka samu rauni.

“Saboda haka da muka lissafin a wannan dan tsakanin, mun samu mutane takwas wadanda suka rasa rayukansu, sai kuma mutane dari da arba’in da takwas da su samu raunuka nau’i daban-daban a hadurra arba’in da tara.”

Bala ya kara da cewa, masu ababen hawa 3,522 ne hukamar tasu ta samu damar kamawa sakamakon laifuka daban-daban da suka aikata. Ya kuma yi kira ga masu ababen hawa musamman masu haya da su daure wajen bin dokokin hanya domin kariyar kansu da kuma lafiyarsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel