Kudin shigo da man fetur cikin Najeriya ya kara kudi – Ibe Kachikwu

Kudin shigo da man fetur cikin Najeriya ya kara kudi – Ibe Kachikwu

Mun samu labari cewa kudin da aka kashewa wajen shigo da tacaccen man fetur har cikin Najeriya ya karu da N35 a halin yanzu. Ministan harkokin man fetur na kasa Dr Ibe Kachikwu ya bayyana wannan.

Ibe Kachikwu yake cewa abin da ake kashewa wajen tace man fetur, har a shigo da shi Najeriya, ya kai kusan N180. Duk da haka dai abin da ake saida litar man fetur a kasar ba ya wuce N145. Hakan na nufin gwamnati ta dauki nauyin tallafi.

Ministan yake cewa abubuwa sun zo wa gwamnatin tarayya da sauki domin da ace ana saida litar man fetur a gidajan man kasar a kan N90 ne, da asusun gwamnatin Najeriya ya koka, yana mai kare kudin tallafin da gwamnate ke biya.

Karamin Ministan na fetur yake cewa dole gwamnati ta bi ta-ka-tsan-tsan game da tallafin man fetur, inda yace za a zauna da duk wadanda ke da ruwa-da-tsaki a kan sha’anin mai a Najeriya kafin gwamnati ta dauki wani mataki.

KU KARANTA: Buhari yayi taron Ministoci da manyan Mukarraban Gwamnati

Kudin shigo da man fetur cikin Najeriya ya kara kudi – Ibe Kachikwu

Dr Emmanuel Ibe Kachikwu yace dole a gyara matatun Najeriya
Source: UGC

Kachikwu yake cewa a 2015 yana cikin mutanen farko da ya tubure ya nuna babu abin da zai sa Najeriya ta rika kashe fiye da Naira Tiriliyan 1.2 wajen biyan tallafin mai don haka ya shawo kan shugaban kasa har aka cire nauyin wannan kudi.

Bayan an cire wannan tallafin mai ne farashin fetur ya tashi a Najeriya zuwa N145. Yanzu kuma dai man ya kara daraja a kasuwannin ketare inda kudin jigilar danyen mai da tacewa da kuma shigo da shi gida ya zarce abin da aka saba biya a baya.

Dr. Kachikwu ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a san yadda za ayi a gyara matatun man gida domin a daina kashe kudi wajen tace mai a waje, sannan kuma ya koka da cewa da-dama na wadanda ake daukewa nauyin kudin mai Attajirai ne.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel