Majalisar wakilai ta mika kudurin neman a bude kwalejin fasaha da kere-kere mallakar Gwamnatin tarayya a Fagge

Majalisar wakilai ta mika kudurin neman a bude kwalejin fasaha da kere-kere mallakar Gwamnatin tarayya a Fagge

-Majalisar wakilai ta nuna amincewarta da a bude kwalejin kimiyya da kere-kere a Fagge, Kano

-Yanzu wannan kuduri zai tafi hannun majalisar dattijai domin suyi tasu bitar suma kafin mika shi zuwa wajen Shugaban kasa

Majalisar wakilai ta gabatar da kudurin neman bude kwalejin kimiyya da kere-kere mallakar Gwamnatin tarayya a Fagge dake jihar Kano a karo na uku. Wannan kudurin dai an gabatar dashi ne a gaban majalisar tun shekarar da ta wuce daga hannun Aminu Suleiman dan majilasa mai wakiltar karamar hukamar Fagge kuma dan jam’iyar APC a karo na farko.

Wannan kudurin kuma ya samu karbuwa a karo na biyu, wanda hakan nema ya bada damar a mika shi zuwa ga kwamitin ilimin gaba da sakandare da kuma asusu na musamman dake taimakawa makarantun (TetFund), wanda shi dan majilasar ke jagoranta.

Majalisar wakilai

Majalisar wakilai
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Yanda aka farmana tare da kashe yan uwanmu, inji wasu jama’ar Nasarawa

Kwamitin bai bata lokaci ba, inda ya zauna ya duba wannan kudurin tare da sauran ma’aikatan sashen ilimi wadanda suka nuna yardarsu na a bude wannan makaranta. A cikin kudirin, an bayyana cewa lallai wannan makaranta idan an budeta zata kara bunkasa ilimin fasaha da kere-kere wanda zai zama doriya akan niyyar gwamnati na samar da tattalin arziki mai karfin gaske kuma abin dogaro.

Suleiman yace idan aka bude wannan makaranta, zata kara ba mutanen wannan karamar hukuma damar samun ilimi na matakin gaba da sakandare, kai harma da sauran kananan hukumomin dake jihar da ma jihohin dake makwabtaka da jihar ta Kano.

A halin yanzu dai, majalisar zata mika wannan kudurin ne zuwa ga majalisar dattijai domin tayi nata bitar itama, daga bisani kuma sai a kai shi gaban shugaban kasa. Dan majalisar ya kara da cewa, yanada tabbacin cewa idan wannan kuduri ya isa gaban Shugaba Buhari zai sanya mashi hannu ba tare da wani tsaiko ba ganin irin cigaba da wannan makaranta zata kawo idan aka budeta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel