Gwamna Ganduje ya rufe wani babban Otel da ake aikata fasadi a jihar Kano

Gwamna Ganduje ya rufe wani babban Otel da ake aikata fasadi a jihar Kano

- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya rufe wani Otel a unguwar Sabon Gari

- Gwamnatin Kano ta rufe Otel din Mbanefo Holiday Inn da ya kasance matattara ta masu aikata fasadi a ban kasa

- A cewar hukumar 'yan sanda, ana aikata miyagun laifuka da suka hadar da karuwanci da kuma cin zarafin bil Adama

Rufe wani Otel na Mbanefo Holiday Inn bisa ga umurnin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya farin ciki a zukata da annashuwa a fuskokin al'umma mazauna yankin Abeokuta da ke unguwar Sabon Gari a jihar Kano.

Otel din Mbanefo da gwamnati ta rufe a jihar Kano

Otel din Mbanefo da gwamnati ta rufe a jihar Kano
Source: UGC

Babban sakataren gwamnatin tarayya na jihar, shi ne ya bayar da sanarwar wannan umurni na rufe babban Otel din da ya kasance matattara ta miyagun ababe masu aikata fasadi a ban kasa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumomin tsaro musamman na 'yan sanda da jami'an hukumar DSS, sun taka rawar gani mai tasirin gaske wajen rufe Otel din na Mbanefo Holiday Inn da ke unguwar Sabon Gari.

Yayin kai simame tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da kuma jagorancin hukumar Hizbah, an samu nasarar cafke ababen zargi 30 masu aikata masha'a da munanan ababe na mugun ji da mugun gani.

KARANTA KUMA: Wani Mutum ya soke 'Dan uwan sa har lahira a jihar Kano

Rahotanni sun bayyana cewa, Otel din Mbanefo ya kasance wani dandali na aikata miyagun laifuka da suka hadar da karuwanci, cin zarafin kananan Yara 'yan Mata da ya sabawa sashe na 44 cikin dokokin hukumar Hizbah ta jihar Kano.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel