Kotu ta bawa EFCC damar kama wasu manyan ministoci biyu a gwamnatin PDP

Kotu ta bawa EFCC damar kama wasu manyan ministoci biyu a gwamnatin PDP

Wata babbar kotun tarayya, karkashin mai shari'a Jastis D. Z. Senchi, da ke zamanta a Jabi, Abuja, ta amince da bukatar hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) na neman a sahale mata ta kama tsohon ministan man fetur, Dan Etete, da tsohon ministan shari'a, Mohammed Adoke, bisa rawar da suka taka a badakalar sayar da rijiyar man fetur ta kamfanin Malabu.

A hukuncin da kotun ta yanke a yau, Senchi ya sahale wa EFCC kama tsofin ministocin biyu duk inda aka gan su.

Etete ya kasance ministan man fetur a gwamnatin PDP a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, yayin da Adoke ya rike mukamin ministan shari'a a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Binciken badakalar sayar da rijiyar man fetur mai lamba OPL 245 ga kamfanin 'Eni and Shell' ya shafi tsofin shugabanni, 'yan siyasa da manajojin kamfanoni a Najeriya da wasu kasashen ketare.

Kotu ta bawa EFCC damar kama wasu manyan ministoci biyu a gwamnatin PDP

Tsohon ministan shari'a; Mohammed Adoke
Source: UGC

Tarihin badakalar sayar da rijiyar man fetur din ya fara ne tun lokacin mulkin Obasanjo, sannan ya ratso har cikin gwamnatin Jonatahan.

Ko a kwanaki biyu da suka wuce, sai da Legit.ng ta kawo muku labarin cewar wasu kungiyoyi hudu da ke rajin kare hakkin bil adama sun rubuta takardar neman hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) da ta kwace wani jirgin sama mallakar tsohon ministar man fetur a lokacin mulkin Obasanjo, Cif Dan Etete.

DUBA WANNAN: Mama Taraba ta temi addu'ar 'yan Najeriya a kan tiyatar da za ai mata a asibiti

Kungiyoyin sun ce jirgin, wanda aka yi kiyasin cewar ya kai dalar Amurka $56m, an saye shi ne da kudin badakalar sayar da rijiyar man fetur mai lamba OPL 245.

Kungiyoyin hudu, a cikin wani jawabi da suka fitar ranar Alhamis ta makon jiya a birnin Milan na kasar Italy, sun bayyana cewar sun samu hujjojinsu ne daga tuhumar badakalar sayar da rijiyar man fetur din da ake yi a kotun kasa da kasa da ke Milan, Italy.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel