Yadda wani Magidanci ya saki matansa 2 a lokaci guda saboda fitina

Yadda wani Magidanci ya saki matansa 2 a lokaci guda saboda fitina

Wata kotun gargajiya dake zamanta a Idi-Ape cikin garin Ibadan na jahar Oyo ta amince ma wani magidanci mai suna Moruff Ajayi ya saki matansa guda biyu, Suliyat da Kudirat sakamakon fitintinu da matayen suke janyo masa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Magidancin ya dade yana zaune da matan nasa, inda ya auro uwargida Suliyat kimanin shekaru ashirin da shida (26) da suka gabata, yayin da ya auro Kudirat kimanin shekaru goma sha shida (16) da suka wuce.

KU KARANTA: Malaman BUK da yan siyasa ne suka kulla magudin da aka yi a zaben Kano – Jega

Da fari dai Maigida Moruff ne da kansa ya shigar da karar matan nasa gaban kotun, inda ya nemi kotu ta kawo karshen zamansa dasu duka sakamakon fitinar da suke janyo masa na yau daban na gobe daban.

Moruff ya shaida ma Alkalin kotun, Moses Oyekanmi cewa “Tun a shekarar 2017 ya fatattki matan nasa daga gidansa saboda tsananin tashin hankali da suke jefashi a dalilin yawan fadace fadace da cacar baki a tsakaninsu, kuma duk kokarin da nayi na sulhuntasu ya ci tura.

“Don haka nake bukatar kotu ta raba aurena dasu duka, sakamakon ni nake daukan nauyin yarana tun bayan dana sallamesu, don haka basu da wata amfani a wajena.” Inji shi.

Bayan jin ta bakin Moruff ne sai Alkali Moses ya amince da kashe auren, sa’annan ya bukaci a kai ma matan nasa kwafin hukuncin daya yanke sakamakon sun ki amsa gayyatar kotu duk kuwa da sammacin da aka kai musu sau uku uku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel