Malaman BUK da yan siyasa ne suka kulla magudin da aka yi a zaben Kano – Jega

Malaman BUK da yan siyasa ne suka kulla magudin da aka yi a zaben Kano – Jega

Tsohon shugaban jami’ar Bayero ta Kano, BUK, kuma tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta wanda duniya ta shaida da gaskiyarsa, Attahiru Jega ya tona asirin yadda yan siyasa suka hada kai da wasu Malaman BUK wajen tafka magudin zabe a jahar Kano.

Legit.ng ta ruwaito Farfesa Attahiru Jega ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen taron kugiyar tsofaffin daliban jami’ar Bayero ta Fullbright, inda yace yan siyasa sun yi amfani da malaman BUK wajen tafka magudin zabe, kuma hakan cin amanar tsarin zabe ne.

KU KARANTA: Buharin dana sani a da, ba shi bane Buharin yanzu – Inji tsohon dogarin shugaba Buhari

Malaman BUK da yan siyasa ne suka kulla magudin da aka yi a zaben Kano – Jega

Attahiru Jega
Source: UGC

Ya kara da cewa su kuma wadannan Malaman jami’an na BUK da aka hada baki dasu wajen tafka wannan almundahana sun ci amanan aikinsu, kuma sun ci zambaci al’umma da hukumar INEC bisa amincewar da hukumar ta nuna musu.

“Ina ganin babbar matsalar da muke fuskanta a dimukradiyyar Najeriya shine yadda wasu masu rike da mukaman iko suke cin zarafin tsarin gaba dayansa, kalli abinda ya faru a zaben Kano, da kuma yadda aka tafka magudi a cikin jami’ar BUK.

“Yan siyasa sun yi amfani da Malaman jami’a wajen cin dunduniyar tsarin zaben gaba daya, tare da yi masa zagon kasa, inda suka tafka magudi iri iri, wanda hakan ya samar da gurguwar zabe, tare da baiwa miyagu daman cigaba da zama akan madafan iko.” Inji shi.

Idan za’a tuna, an samu korafe korafe game zaben gwamnan jahar Kano, musamman zaben maimaici da aka yi bayan rashin samun tabbataccen wanda ya samu nasara a zaben a karon farko tsakanin Gwamna Ganduje da Abba Yusuf.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel