Aiki na kyau: Dakarun Sojin sama na cigaba da aman wuta akan yan bindigan Zamfara

Aiki na kyau: Dakarun Sojin sama na cigaba da aman wuta akan yan bindigan Zamfara

Dakarun rundunar Sojan na musamman sun tarwatsa wasu gungun yan bindiga da suka kaddamar da hare hare a kauyukan Rafi da Dola dake cikin lardin Mada na karamar hukumar Gusau ta jahar Zamfara a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.

Kaakakin rundunar, Komodo Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace sun samu bayanai dake nuna yan bindigan sun fara tattaruwa a kauyukan Rafi da Dola da nufin kai musu hari, hakan tasa suka garzaya don fafatawa dasu.

KU KARANTA: Buharin dana sani a da, ba shi bane Buharin yanzu – Inji tsohon dogarin shugaba Buhari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Daramola yana cigaba da fadin ba tare da bata lokaci ba suka tura da wasu rukunin dakarun Sojoji na musamman, wanda suka tarwatsa shirin yan bindiga, har ma suka kashe guda biyu daga cikinsu, yayin da sauran suka ranta ana kare dauke da munanan raunuka.

Sai dai kaakakin yace Sojojin basu yi kasa a gwiwa ba, inda suka bi sawun sauran yan bindigan da suka arce zuwa dazuka, lunguna da sakon dake makwabtaka da kauyukan don kare aukuwar wani harin ba zata daga yan bindigan.

Daga karshe ya bada tabbacin rundunar Sojan sama, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro zasu yi iya bakin kokarinsu don ganin sun cigaba da zage damtse a yakin da suke yi da yan bindiga har sai sun kawo karshensu kwata kwata.

A wani labarin kuma, uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta kai ma jama’an da matsalar tsaro a jahar Zamfara ta shafa dauki, inda ta raba musu tallafi kayayyaki don rage musu radadin mawuyacin halin da suka tsinci kawunansu a ciki.

Aisha ta yi wannan aikin alheri ne ta hannun gidauniyarta mai suna Future Assured, inda ta raba tallafin kayan abinci da sutura ga yan gudun hijira da adadinsu ya kai mutum dubu biyar (5,000).

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel