Wani Mutum ya soke 'Dan uwan sa har lahira a jihar Kano

Wani Mutum ya soke 'Dan uwan sa har lahira a jihar Kano

Wani Matashi mai shekaru 30 a duniya mazaunin unguwar Sauna a karkashin karamar hukumar Nasawara ta jihar Kano, Tasi'u Iliyasu, ya daba wa dan uwan sa wuka, Abba Sule, inda ya hallaka shi murus har lahira.

Wani Mutum ya soke 'Dan uwan sa har lahira a jihar Kano

Wani Mutum ya soke 'Dan uwan sa har lahira a jihar Kano
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Abba ya riga mu gidan gaskiya nan take yayin da dan uwan sa ya yi masa aika-aika da kawowa yanzu bincike bai kai ga sanin dalilin wannan danyen hukunci ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar Kano Chronicles cikin birnin Kano a ranar Talata.

KARANTA KUMA: Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Fayemi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti

Kiyawa ya ce Iliyasu ya yi tarayya da wani Mutum mai sunan Magaji wajen aikata mummunar ta'adar da misalin karfe 8.20 na daren ranar Lahadin da ta gabata. Sai dai kawowa yanzu ababen zargin biyu sun danna layar zana.

Kamar yadda babban jami'in dan sandan ya bayyana, ana ci gaba da gudanar da bincike domin bankado miyagun mutanen biyu domin su fuskanci hukunci daidai da abin da suka aikata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel