Bayan 'yan matsalolin da shafin ya fuskanta, yanzu haka shafin hukumar kwastan ya fara aiki

Bayan 'yan matsalolin da shafin ya fuskanta, yanzu haka shafin hukumar kwastan ya fara aiki

- An bude shafin yanar gizo na hukumar kwastan

- Za a rufe shafin nan da mako uku masu zuwa

Hukumar kwastan ta Najeriya (NCS) ta ce yanzu haka shafinta na yanar gizo ya bude domin daukar ma'aikata 3,200, wanda za a fara yau Larabar nan.

Majiyarmu LEGIT.NG ta fuskanci cewa shafin hukumar na yanar gizo ba ya budewa a jiya da daddare.

Bayan haka, jami'in hulda da jama'a na hukumar, Joseph Attah ya ce yanzu shafin ya fara, inda mutane da yawa har sun fara cika fom din. A lokacin da ya ke amsa tambayar manema labarai akan matsalar da ta saka shafin ya daina aiki a daren jiya, Attah ya ce hakan ya faru ne saboda yawan mutane da suka bude shafin.

Bayan 'yan matsalolin da shafin ya fuskanta, yanzu haka shafin hukumar kwastan ya fara aiki

Bayan 'yan matsalolin da shafin ya fuskanta, yanzu haka shafin hukumar kwastan ya fara aiki
Source: Depositphotos

Majiyarmu LEGIT.NG ta tabbatar da cewa shafin yana aiki a daidai lokacin da ta aiko da wannan rahoton.

Jiya Talata ne hukumar kwastan din ta sanar da al'umma cewa za ta dauki ma'aikata 3,200 a wannan karon.

KU KARANTA: Atiku ya gabatarwa da kotu shaidar da yake da ita akan magudin zabe

Mataimakin shugaban hukumar kwastan mai rikon kwarya, Umar Sanusi shi ne ya bayyana hakan jiya a Abuja.

Sanusi ya bayyana cewa za su dauki mutane 800 wadanda zasu cike gurbi na Superitendent Cadre, sannan mutane 2,400 za a dauke su a matsayin Customs Inspector da Customs Assistant Cadre.

Ya ce shafin hukumar na yanar gizo zai fara aiki daga karfe 12 na daren jiya Talata sannan za a rufe shafin bayan sati uku da bude shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel