Shugabancin majalisa ta 9: Baza muyi aiki tare da PDP ba, Oshiomole ya jaddada

Shugabancin majalisa ta 9: Baza muyi aiki tare da PDP ba, Oshiomole ya jaddada

-Ya zama dole mu guji sake aukuwar abinda ya faru a 2015, inji Oshiomole

-Jam'iyar APC itace da rinjaye a majalisar wakilai ta 9 da mambobi 223 cikin 360 dake akwai

Shugaban jam’iyar APC na kasa, Adams Oshiomole ne yayi wannan furucin a daren jiya yayinda ya bayyana jam’iyar ta PDP a matsayin shaidaniyar jam’iya. Yace jami’iyar APC ita ce ke da rinjaye a duka sassa guda biyu na majalisar a don haka suna da wadanda zasu iya jan akalar majalisar ta 9 ba tare da sun hada hannu da PDP ba.

Oshiomole ya fadi hakan ne a fadar Shugaban kasa, inda Shugaba Buhari ya karbi bakuncin zababbun yan majilasar wakilai na jam’iyar APC akan halartar wata liyafa da aka shirya dominsu. A daidai wannan lokacin ne Oshiomole ya gabatar da Femi Gbajabiamila a matsayin wanda jam’iyar ta amince dashi matsayin da ya zamo kakakin majalisa ta 9.

Adams Oshiomole

Adams Oshiomole
Source: UGC

KU KARANTA:Wata mata ta gurfana gaban kotu saboda ta doki yarinya mai shekara 9 da ice mai ci da wuta

Shugaban jam’iyar ya kara da cewa idan mutum kaga an zabe shi, to hakika an yarda da shine kan cewa zai iya yin kyakkyawan jagoranci. Ana su bangaren kuwa zababbun yan majalisar sun bada tabbacin cewa zasu marawa shugaban kasa baya domin cigaban wannan kasa tamu.

“Hakika ina da yakinin cewa wadannan yan majalisa baza su kawo mana cikas ba kamar yanda muka kasance muna samu daga wurin Bukola Saraki da Yakubu Dogara wanda yayi matukar kawo ma hukumar zartarwa matsaloli da dama. Ya kara da cewa duba ga rinjayen da jam’iyar APC take dashi a majalisar wakilai inda muke da mambobi 223 cikin 360 bamu da bukatar sai PDP ta sanya mana hannu kafin mu gudanar da wani jagoranci.”

Bugu da kari, a rayuwa ana yiwa mutum uzuri idan yayi kuskure ne sau daya kacal, yayinda sake maimita kuskuren shine ke zama laifi. Don haka a shirye muke tsaf domin gujewa sake aukuwar kuskuren da mukayi a 2015 a wannan lokacin, tabbas mun gane kurenmu kuma munyi shirin yin gyara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel