Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Fayemi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Fayemi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti

A ranar Laraba 17 ga watan Afrilu, kotun koli ta Najeriya ta tabbatar da nasarar gwamna Kayode Fayemi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar a ranar 14 ga watan Yulin shekarar 2018 da ta gabata.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kotun ta tabbatar da nasarar Fayemi biyo bayan korafin da Cif Segun Oni ya shigar, abokin adawar sa tun a yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da aka gudanar gabanin babban zaben gwamnan jihar.

Gwamnan jhar Ekiti; Kayode Fayemi

Gwamnan jhar Ekiti; Kayode Fayemi
Source: Depositphotos

Cikin korafin da Cif Oni ya shigar, ya kalubalanci sakamakon zaben da cewa Mista Fayemi ba ya da cancantar tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar bisa ga ka'ida ta sabawa wasu dokoki na shari'a da hukunce-hukuncen zabe.

Cif Oni wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Ekiti, yayin shigar da korafin sa ya ce bisa ga sabawa doka ta hukunce-hukuncen zabe, Fayemi bai ajiye aikin sa ba na kujerar Ministan hako ma'adanan kasa kwanaki 30 gabanin zaben fidda gwanin takara.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'yan kungiyar asiri 151 a jihar Anambra

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa wanda ya zo na biyu yayin zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar Ekiti, ya nemi kotu ta yi watsi da cancantar takarar Fayemi sakamakon binciken da tsohon gwamna Ayo Fayose ya aiwatar a kansa.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatarwa da kotu kwararan shaidu masu tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel