Wani dan majalisa ya bayyana kudurinsa na fitowa takarar kakakin majalisa

Wani dan majalisa ya bayyana kudurinsa na fitowa takarar kakakin majalisa

Jim kadan bayan shugabannin jam'iyyar APC sun fitar da zabin su a majalisar wakilai, sai ga wani dana majalisar wakilai ya fito ya nuna rashin aimncewar shi akan hakan, inda ya bayyana cewa bai ga dalilin da yasa ake ware yankin arewa ta tsakiya ba a majalisar Najeriya

A yau Larabar nan ne wani dan majalisar wakilai na tarayya, John Dyegh (APC Binuwai) ya bayyana kudurin sa na fitowa takarar kakakin majalisa.

Hakan ya biyo, jim kadan bayan shugabannin jam'iyyar APC sun tsayar da Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin zabi gareta na wanda zai shugabanci majalisar wakilan.

Wani dan majalisa ya bayyana kudurinsa na fitowa takarar kakakin majalisa

Wani dan majalisa ya bayyana kudurinsa na fitowa takarar kakakin majalisa
Source: UGC

Dyegh, wanda ya sanar da hakan a babban birnin tarayya Abuja, ya bayyana biyayyar shi ga jam'iyyar APC, amma ya kara da cewa bai ga dalilin da yasa za a bawa yankin kudu maso yamma wannan mukami ba bayan sune suke da mataimakin shugaban kasa.

KU KARANTA: Atiku ya gabatarwa da kotu shaidar da yake da ita akan magudin zabe

"Ina sanar da kudurina na fitowa takarar kakakin majalisar wakilai. Na yanke shawarar hakan ne bayan na yi la'akari da yadda jam'iyya ta juyawa yankin arewa ta tsakiya baya ba tare da gabatar da wani kwakkwaran dalili ba," in ji shi.

A jiya ne dai shugabannin jam'iyyar APC suka tsayar da Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin zabi garesu na wanda zai zama kakakin majalisar wakilai na tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel