Shugaba Buhari ya shiga taro da 'yan majalisar sa da ministoci 21

Shugaba Buhari ya shiga taro da 'yan majalisar sa da ministoci 21

- Yanzu yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wani taron gaggawa da 'yan majalisar sa

- Sai dai kuma an nemi mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ko sama ko kasa an rasa a wurin taron

A halin yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a fadar shi da ke babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya jagoranci taron a satin da ya gabata bai samu damar halartar taron ba.

Shugaba Buhari ya shiga taro da 'yan majalisar sa da ministoci 21

Shugaba Buhari ya shiga taro da 'yan majalisar sa da ministoci 21
Source: Facebook

Mun samu labarin cewar an fara gabatar da taron jim kadan bayan isowar shugaban kasar majalisar da misalin karfe 10:59 na rana.

KU KARANTA: Atiku ya gabatarwa da kotu shaidar da yake da ita akan magudin zabe

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Gida Mustapha, shugaban ma'aikata na tarayya, Abba Kyari, mai bada shawara a fannin tsaro, Babagana Monguno da ministoci 21 ne suka halarci taron.

A karshen taron, za a sanar da manema labarai ainahin abinda aka tattauna a taron.

Kamar kullum dai shugaban kasar ya saba gabatar da taron kowanne sati, domin jin halin da kasar ta ke ciki sannan kuma a nemo mafita akan wasu abubuwan da suke damun kasar.

Nan ba da jimawa ba zamu kawo muku ainahin abubuwan da aka tattauna a taron na yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel