Harin Nasarawa: Al-Makura ya baiwa jami’an tsaro kwana bakwai su nemo masu laifin

Harin Nasarawa: Al-Makura ya baiwa jami’an tsaro kwana bakwai su nemo masu laifin

-Al-Makura ya lashi takobin kawo karshen ta'addanci a jihar Nasarawa

-Akwai bukatar jami'an tsaro su mike tsaye domin fada da yan ta'adda, kira daga bakin Tanko Umar Al-Makura

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Al-Makura ya baiwa jami’an tsaro kwana bakwai da su nemo wadanda suka aikata ta’addanci da ya auku a kauyen Numa Kochu da ke karamar hukumar Akwanga wanda yayi sanadiyar rayukan mutane 16.

Gwamnan ya bada wannan umurnin ne yayinda ya kai ziyara ga wadanda suka samu rauni sakamakon faruwa wannan abu wadanda ke jinya a babban asibitin Akwanga ranar Talata. Yace, “Nayi muku alkawarin cewa gwamnatinmu zatayi duk abin da ya dace domin kawo karshen aukuwar ire-iren wadannan ta’addacin a jiharmu. Jiharmu ta kasance inda ake rayuwa cikin tsanin zaman lafiya da kwanciyar hakali musamman cikin shekaru uku da suka gabata.

Umar Al-Makura

Umar Al-Makura
Source: Twitter

KU KARANTA:Wata mata ta gurfana gaban kotu saboda ta doki yarinya mai shekara 9 da ice mai ci da wuta

“Ya zama dole mu zauna domin tattaunawa da jami’an tsaro na wannan jiha tamu, na riga da na baiwa jami’an kwana bakwai domin su nemo wadanda suka aikata wannan mummunan ta’adi kana kuma a gurfanar dasu gaban shari’a domin su fuskanci hukuncin da ya dace da su.”

Gwamnan ya sake yin kira ga jami’an tsaro dake yankin da wannan abu ya faru na su kara zage dantse wajen tsaurara tsaro. Kana kuma ya umurcesu da su kafa dan sansani a kusa da wurin saboda ya zama an kara inganta tsaro a wannan wurin da abin ya auku.

A karshe kuwa, ya bada tabbacin cewa gwamnati zata daukin nauyin maganin wadanda suka jikkata da suke asibiti da kuma na gudanar da birne wadanda suka rasu, kana kuma zata bada kayan agaji zuwa ga wannan kauyen da aka kai harin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel