Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'yan kungiyar asiri 151 a jihar Anambra

Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'yan kungiyar asiri 151 a jihar Anambra

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Anambra, ta ce ta samu nasarar cika hannun ta dumu-dumu da miyagun 'yan kungiyar asiri kimanin 151 da suka afka tarko bayan ta yi masu tarnaki a ramukan su na buya.

Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'yan kungiyar asiri 151 a jihar Anambra

Hukumar 'Yan sanda ta cafke 'yan kungiyar asiri 151 a jihar Anambra
Source: UGC

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, hukumar 'yan sanda ta samu nasarar cafke 'yan kungiyar asiri 151 a jihar Anambra biyo bayan matsin lamba na sintiri da kai komo da ta dabbaka a tsakanin ranar 1 zuwa 16 ga watan Afrilun 2019.

SP Muhammad Haruna, kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganarwar sa da manema labarai a ranar Talatar da ta gabata cikin birnin Awka.

Babban jami'in 'yan sandan ya ce hukumar ta kuma samu nasarar cafke miyagun makamai da wasu kayan maye da ake zargin ciyawa ce ta tabar wiwi. Kazalika SP Haruna ya ce cikin ababen zargin da aka cafke akwai kimanin Yara 20 da hukuncin doka bai rataya a wuyan su ba.

KARANTA KUMA: Sarkin Musulmi ya fadakar da gwamnatin tarayya a kan sabanin siyasa da addini

Yayin bayar da tabbacin ci gaba da bincike a kan miyagun ababe domin gurfanar da su a gaban Kuliya, kakakin 'yan sandan ya nemi hadin kan al'umma wajen shigar da rahoton duk wasu ababe na rashin yarda da ke aukuwa a zamantakewar su.

Cikin wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, a ranar Lahadin da ta gabata rikicin makiyaya da manoma ya salwantar da rayukan Mutane 16 tare da raunata kimanin Mutane 14 a kauyen Numa da ke karkashin karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel