JAMB 2019: An kama yara biyu na wani mai cibiyar zana jarabawar saboda magudi

JAMB 2019: An kama yara biyu na wani mai cibiyar zana jarabawar saboda magudi

-Karyar wasu yara ta kare yayinda suka shiga hannu sakamakon magudin jarabawa

-Sama da mutane dari ne hukumar JAMB ta samu nasarar kamawa kawowa yanzu da laifin magudin jarabawa

Hukumar tsara jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare wato JAMB ta samu nasarar damke yara biyu na wani mutum dake da mallakar cibiyar zana wannan jarabawa bisa ga zargin aikata magudin jarabawa.

Yan jarida sun shaida mana cewa an kama wadannan yara ne yayinda jagoran wannan hukumar mai suna, Farfesa Ishaq Oloyede ke gudanar da kewayawa domin ganin yanda jarabawar ke tafiya a ranar Talata a jihar Legas.

Shugaban hukumar JAMB

Shugaban hukumar JAMB
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Wata mata ta gurfana gaban kotu saboda ta doki yarinya mai shekara 9 da ice mai ci da wuta

Oloyede yace, “Sama da mutane dari ne aka samu nasarar kamawa kawo yanzu da laifin magudin jarabawa inda kuma hukumar bata yi wata wata ba ta mikasu hannun jami’an tsaro. Kana kuma ya kara da cewa kimanin mutane sama da miliyan daya kawowa yau suka rubuta jarabawar.

Haka zalika, wadannan yaran dai sun kasance suna daukan hoton tambayoyin ne a wayarsu inda suke turawa zuwa wani wurin domin a basu amsoshin wadannan tambayoyin kai tsaye. “Mun kasance muna gudanar da yawon duba yanda jarabawar ke wakana kamar yanda muka saba zuwa ko wace cibiyar zana jarabawar, a daidai wannan lokacin ne kuma labari yazo mana cewa ana tafka magudi a ita wannan cibiya.”

“Sun kasance suna yin abin nasu ne da tunanin cewa ai hukumarmu bata da masaniya akai saboda sun katse gaba daya kamarorin tonon asiri dake dakin jarabawar, sai dai basu san cewa muna da hanyar da zamu iya gane abinda ke faruwa a duk cibiyoyin jarabawar dake fadin kasar nan tun daga babban ofishinmu dake Abuja.”

“Tabbas wannan cibiyar an gama rubuta jarabawa a cikinta, wadanda suka rage zasu rubuta a nan zamu canza musu wuri. A halin yanzu dai an rufe wannan cibiya kana kuma an dakatar da ita na gaggawa daga cigaba da duk wani sha’anin jarabawar. Babu wanda zai sake rubuta jarabawa a nan,” ya kara fadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel