IDP: Gwamnati ta tallafawa Marayu da gajiyayyu da abinci a Kwara

IDP: Gwamnati ta tallafawa Marayu da gajiyayyu da abinci a Kwara

Jaridar nan ta The Nation ta kasar nan ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta agazawa masu gudun hijira da kuma wadanda su ke zaune a gidajen Marayu da kayan tallafi da kuma abinci a jihar Kwara.

Jami’an Kwastam masu yaki da fasa-kauri a cikin Najeriya, su ne su ka rabawa marasa karfin wannan kayan abinci, a madadin gwamnatin tarayyar Najeriya. Babban Jami’in Kwastam na kasar, Yakubu Salihu ya bayyana wannan.

Kayan da aka rabawa Marayun da sauran wadanda ke fake a sansanin gudun hijirar, duk kaya ne da hukumar ta karbe daga hannun masu shigo da kayan da aka haramta ko kuma daga hannun masu yunkurin bi ta barayin hanyoyi.

KU KARANTA: Ni wani daban na sani ba wannan Buharin ba inji tsohon Dogarinsa

IDP: Gwamnati ta tallafawa Marayu da gajiyayyu da abinci a Kwara

Gwamnatin Tarayya ta ba mutanen IDP gudumuwa a Kwara
Source: Facebook

Salihu yake cewa sun raba wannan kaya ne bayan wani umarni da su ka samu daga fadar shugaban kasa, inda aka nemi a dauki kayan da aka tsare, a rabawa gajiyayyu da ke cikin sansanin IDP da kuma wadanda ke gidajen Marayu.

Yakubu Salihu wanda shi ne shugaban wannan kwamiti na musamman da aka kafa domin rabawa marasa hali abinci, ya bayyana cewa sun fara wannan aiki ne daga shiyyar Kudu watau tun daga Legas, Osun, Oyo da kuma Ogun.

Yanzu dai wannan aiki ya iso jihar Kwara domin ganin an rage cunkoson da ke cikin dakunan ajiye kaya na hukumar. Jami’in hukumar yake fadawa manema labarai cewa sai sun tabbatar da gidajen Marayu sannan su ke raba kaya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel