Sarkin Musulmi ya fadakar da gwamnatin tarayya a kan sabanin siyasa da addini

Sarkin Musulmi ya fadakar da gwamnatin tarayya a kan sabanin siyasa da addini

Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku, ya nemi gwamnatin tarayya da ta shimfida ingatattun tsare-tsare wajen warware takaddama ta sabanin siyasa da kuma addini a kasar nan.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku, ya yi kira na neman gwamnatin tarayya ta shiga cikin lamari domin warware takkadama ta sabani a tsakanin siyasa da addini da ke ci gaba da kunnowa a fadin kasar nan.

Sarkin Musulmi ya fadakar da gwamnatin tarayya a kan sabanin siyasa da addini

Sarkin Musulmi ya fadakar da gwamnatin tarayya a kan sabanin siyasa da addini
Source: Twitter

Sarkin Musulmi ya yi kiran ne a ranar Talatar da ta gabata cikin garin Abuja yayin bikin kaddamar da wata mujalla ta kungiyar kare hakkin Musulmi MURIC mai shafi 240 wadda jagoran kungiyar ya wallafa, Farfesa Ishaq Akintola.

Sultan na Sakkwato wanda Sarkin Keffi kuma shugaban jami'ar jihar Nasarawa ya wakilta, Dakta Shehu Chindo Yamusa na uku, ya bayyana damuwa a kan yadda ake ribatar addini ta hanyar rashin dace da ke haifar da barazana ta zaman lafiya da rashin hadin kai a kasar nan.

KARANTA KUMA: Rayuka 16 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa

A yayin fadarkar da kungiyar MURIC a kan jajircewa wajen umurni da adalci, zaman lafiya da kuma hadin kai, Sultan ya nemi gwamnatin tarayya ta kafa wani ginshiki mai warware sabani a tsakanin siyasa da kuma addini domin fidda kasar nan zuwa tudun tsira.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel