Abubaka Malami SAN ne ke dawo da hannun agogo baya - Say No Campaign

Abubaka Malami SAN ne ke dawo da hannun agogo baya - Say No Campaign

- Ana yawan zargin Ministan shari’an Najeriya da yin ba daidai ba a Gwamnatin Buhari

- Yanzu haka wata kungiya ta Say No Campaign tace Ministan na kawowa Buhari cikas

- Kungiyar take cewa Abubakar Malami barazana ne ga yaki da rashin gaskiyar da ake yi

Abubaka Malami SAN ne ke dawo da hannun agogo baya - Say No Campaign

Ministan shari’a yana yi wa Buhari zagon-kasa inji wata Kungiya
Source: Facebook

Mun ji cewa wata kungiya mai zaman kan-ta a Najeriya mai suna Say No Campaign ta zargi Ministan shari’a watau babban Lauya Abubakar Malami SAN da kawo cikas wajen yakin da gwamnatin nan ta ke yi da rashin gaskiya.

Shugaban kungiyar ta Say No Campaign, Mista Ezenwa Nwagwu, ya jefa wannan zargi ne a lokacin da aka shirya wani zaman a musamman domin tattaunawa game da sha’anin yaki da rashin gaskiya da ofishin Ministan shari’a.

KU KARANTA: Atiku ya mikawa kotu bakandamiyar shaidar da ke nuna ya doke Buhari

An yi wannan zama ne a Ranar Talata 16 ga Watan Afrilu a cikin Abuja. Nwagwu yake cewa Ministan shari’ar ya zama ala-ka-kai wajen kokarin da shugaba Buhari yake yi, a maimakon ace ya zama shi ne babban mai bada goyon baya.

Ezenwa Nwagwu yayi kira na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bi a hankali, ya nada mutane masu mutunci a gwamnatinsa wannan karo, wanda za su taimaka masa, ba wadanda za su rika tadiye masa kafa ba.

Kungiyar tana ganin cewa Abubakar Malami bai taimaka wajen ganin an yaki barayin Najeriya yadda ya dace ba. Wadanda su ka yi magana a wajen taron su na ganin duk da nasarar da aka samu, Minista Malami ya rika kawo cikas.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel