Nnamdi Kanu ya kara tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa Atiku dan Kamaru ne

Nnamdi Kanu ya kara tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa Atiku dan Kamaru ne

- Nnamdi Kanu ya kara tabbatar da cewa Atiku ba dan Najeriya ba ne

- Ya ce bai kamata a baiwa duk dan jihar Adamawa wanda aka haifa daga shekarar 1940 zuwa 1960 tikitin takarar shugaban kasa ba

Shugaban 'yan kungiyar masu radin kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya ce zargin da jam'iyyar APC ta ke yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, na cewa shi dan kasar Kamaru ne, ya tabbatar da ikirarin da ya yi kwanakin baya akan Atikun.

Da yake jawabi ga 'yan kungiyar ta shi ta gidan radiyon Biafra, Kanu ya ce: "Jam'iyyar APC ta shaidawa kotu cewa Atiku ba dan Najeriya ba ne, hakan yana nuni da cewa duk abinda na fada a gidan radiyo Biafra gaskiya ne. Ya na iya zama mutane su kyamaci abinda na fada ko ma su ki yarda da abinda na ce a farko, amma a hankali gashi nan gaskiya ta fara fitowa.

Nnamdi Kanu ya kara tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa Atiku dan Kamaru ne

Nnamdi Kanu ya kara tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa Atiku dan Kamaru ne
Source: UGC

"Kamar yadda kowa ya ke gani, an bayyana cewa babu shakka, idan har kana so ka zama shugaban kasar Najeriya, dole ne a haifeka a Najeriya. A lokacin da aka haifi Atiku Abubakar a jikin takardar haihuwar shi ya nuna kasar Kamaru ne."

Kanu ya bayyana cewa tsarin mulkin kasar nan na 1999, kamar yadda aka bayyana, ba shi da wani tsari saboda wadanda suka kirkiro shi ba wasu masana ba ne na tsarin mulki.

A cewarsa, hujjar da mutane ke bayarwa cewa Atiku dan Kamaru ne ba gaskiya ba ce, domin kuwa da dan Kamaru ne da bai zama shugaban Kwastam na kasa ba, sannan da bai zama mataimakin shugaban kasa ba.

Kanu ya ce: "Gaskiyar maganar ita ce Alhaji Atiku Abubakar ya zama dan Najeriya ne saboda kundin tsarin mulki da aka gabatar a ranar 11 ga watan Fabrairun shekarar 1961. Ba a haife shi a Najeriya ba, amma ya zama dan Najeriya sakamakon wani tsari da kasar Birtaniya ta kawo, wanda ta bai wa mutanen kasar Kamaru da mutanen jihar Adamawa damar zabar kasar da suke so su zauna.

KU KARANTA: El-Rufai ya kori ma'aikatan sa

"Lokacin da na fara gabatar da wannan batun, kowa ya yi watsi dashi ciki kuwa harda hukumar zabe ta kasa, a lokacin ba wai na yi batun dan na nuna cewa Atiku ba dan Najeriya ba ne. Na yi batun ne saboda ina so nuna cewa ba wai laifi bane dan 'yan kugiyar IPOB sun nuna cewa suna so ayi gyara a kundin tsarin mulki da zai basu damar ware kasarsu.

Shugaban 'yan kungiyar Biafra ya bayyana cewa idan za a bi ka'ida a Najeriya, duk wani wanda aka haifa a jihar Adamawa daga shekarar 1946, lokacin da aka haifi Atiku kenan, zuwa shekarar 1960, bai kamata ya fito takarar shugaban kasa a Najeriya ba.

Ya kara da cewa: "An haifi Atiku Abubakar a ranar 25 ga watan Nuwambar shekarar 1946, a garin Jada, wanda ke cikin arewacin kasar Kamaru a da. Gaskiyar magana shi dan kasar Kamaru ne, amma ya zama dan Najeriya ta hanyar tsarin da kasar Birtaniya ta kawo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel