Nnamdi Kanu ya baiwa Atiku shawara ya sanya Buhari ya je ya yi gwajin DNA

Nnamdi Kanu ya baiwa Atiku shawara ya sanya Buhari ya je ya yi gwajin DNA

- Nnamdi Kanu ya bukaci Atiku Abubakar ya tilasta shugaban kasa Buhari ya je ya yi gwajin DNA, wanda zai tabbatar da cewa shi dan Najeriya ne

- Kanu ya ce idan har gwajin ya tabbatar da cewa Buhari dan Najeriya ne to ya yi alkawarin za su daina ta da zaune tsaye

Shugaban kungiyar Biafra, (IPOB), Nnamdi Kanu, wanda yanzu haka gwamnatin Najeriya ke neman shi ruwa a jallo, ya bai wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wata muhimmiyar shawara.

Kanu wanda ya yi magana a gidan rediyon Biafra, ranar Lahadin nan da ta gabata, ya bukaci Atiku ya sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je ya yi gwajin DNA don min tabbatar da asalinsa.

Gwajin DNA ya kunshi bayanan kwayoyi da bayanan kowane mutum a duniya.

Nnamdi Kanu ya baiwa Atiku shawara ya sanya Buhari ya je ya yi gwajin DNA

Nnamdi Kanu ya baiwa Atiku shawara ya sanya Buhari ya je ya yi gwajin DNA
Source: Depositphotos

Ya ce, "Zan ba wa Atiku shawara, akan zaben da aka gabatar domin shaidu sun nuna cewa Atiku ne ya lashe zaben shugaban kasa amma jam'iyyar APC ta hana shi kujerar.

"Tsakanin Atiku da Buhari, Atiku ne kawai dan Najeriya, Buhari dan Sudan ne. Atiku ba a Najeriya aka haife shi ba, amma ya zama dan Najeriya ta hanyar wani tsari da kasar Birtaniya ta kawowa kasar Kamaru da jihar Adamawa, inda ya zabi yana so ya zama dan Najeriya. Amma Buhari ba dan Najeriya ba ne. Saboda haka Atiku ya bukaci Buhari ya je ya gabatar da gwajin DNA, ni kuma na yi alkawarin idan har DNA ya tabbatar da cewa Buhari dan Najeriya ne, zan daina kokarin da nake na kafa kasar Biafra.

KU KARANTA: El-Rufai ya kori ma'aikatan sa

"Bayan haka, maganar da jam'iyyar APC ta kai kotu, ya tabbatar da cewa duk abinda na ke fada a gidan rediyon Biafra gaskiya ne.

"Na san a farko dole mutane za su karyata ni, amma gashi nan a hankali gaskiya ta fara bayyana. Yanzu lokaci ne da Atiku da 'yan kungiyar shi za su yi amfani da damar su akan Jibril na Sudan," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel