2019: Gwamnan Kaduna ya fatattaki dukkanin Mukarraban sa

2019: Gwamnan Kaduna ya fatattaki dukkanin Mukarraban sa

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu ya salami dukkanin wadanda ke rike da mukaman siyasa, ya bukaci da su gabatar da takardun ajiye aiki zuwa ranar 30 ga watan Afrilu, 2019.

Yace su mika dukkanin takardun ajiye aiki zuwa ga babban sakataren gwamnati.

Babban hadimin gwamnan a kafofin watsa labarai, Samuel Aruwwa ya bayyana hakan a wata sanarwa ga manema labarai a jihar.

2019: Gwamnan Kaduna ya fatattaki dukkanin Mukarraban sa

2019: Gwamnan Kaduna ya fatattaki dukkanin Mukarraban sa
Source: Depositphotos

Yayi bayanin cewa gwamnan zai aiwatar da hakkin da kundin tsarin mulki ta bashi wajen yanke shwara akan sake nadin nasu.

Ya kuma ba ma’aikatar kudi na jihar Kaduna da ta biya duk wani kudi akan lokaci sannan ta sasanta duk wasu matsaloli.

KU KARANTA KUMA: Mutum 7 sun mutu, 58 sun jikkata a hatsarin mota a Kwara

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Yan sanda a Zaria sun kama wasu yan fashi biyu da suka addabimasu mota a yankin Dumbin Rauga da ke hanyar babbar titin Zaria-Kaduna.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya tabbatar da kamun, inda yace an samo bindigar AK 47,alburusai da kuma layoyi daga yan fashin.

Da farko, wata majiya ta yan sanda a Zaria tace wasu tawagar yan sanda da suka tafi sintiri ne suka kama yan ta’addan bayan sun shige daji a lokain da suka hango motarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel