Janar Buratai yana neman hadin-kan Sarakuna wajen shawo kan matsalar tsaro

Janar Buratai yana neman hadin-kan Sarakuna wajen shawo kan matsalar tsaro

Mun ji labari cewa Mai Martaba Sarkin Kasar Benin watau OBA na Benin, Omo N’Oba Ewuare II, ya koka da halin da sha’anin tsaro ya shiga a halin yanzu, amma yana mai yabawa kokarin jami’an tsaro.

Mai Martaba Sarki Omo N’Oba Ewuare II ya jinjinawa Dakarun Sojojin Najeriya ne a lokacin da shugaban hafsun sojin kasar Laftana Janar Tukur Yusuf Burutai ya kawo masa ziyarar ban girma har cikin fadar sa a cikin makon nan.

Sarkin na Benin yake cewa sojoji su na kokari wajen ganin an samu zaman lafiya a fadin kasar nan. Sarkin ya kuma yi amfani da wannan dama inda yayi wa Rundunar sojin ta’aziyyar rashin Jami'an ta da tayi ‘yan kwanakin nan.

KU KARANTA: Wani shehin Malami ya fadawa Buhari gaskiya a kan rikicin Zamfara

Janar Buratai yana neman hadin-kan Sarakuna wajen shawo kan matsalar tsaro

Hafsun Sojin Najeriya ya kai wa Oba na Kasar Benin ziyara
Source: Twitter

Idan ba ku manta ba, kwanan nan ne wasu Sojojin Najeriya su ka mutu wajen artaba da Mayakan ta’adda na Boko Haram. Omo N’Oba Ewuare na II yayi wa babban Sojan kasan Najeriya ta’aziyyar wannan rashi da yayi.

Haka zalika babban Sarkin kasar ya yabawa Tukur Buratai na nada Yaron su watau Birgediya Janar C. Osa Omoregie a matsayin babban kwamdan sojojin Najeriya. Sarkin yace Kasar Edo ta ji dadin wannan karamci da aka yi wa na ta.

KU KARANTA: Rashin aikin yi: Sarkin Kano ya bada shawarar a koma gona a Arewa

Oba Ewuare II a jawabin na sa ya koka da halin da tsaro ya shiga a Najeriya inda yace abubuwa sun tabarbare. Mai martaban dai ya bayyana cewa a shirya yake ya ba jami’an sojoji duk irin gudumuwar da su ke bukata a cikin kasar sa.

Janar TY Buratai a na sa bangaren, ya bayyanawa Sarkin cewa ya zo jami’ar Igbinedion ta jihar ne domin gabatar da lacca don haka yaga akwai bukatar ya kawowa Mai martaba ziyara ta musamman domin a hada karfi da karfe.

Tukur Buratai yake cewa tasirin Sarakunan gargajiya wajen inganta tsaro ya wuce yadda mutane su ke tunani. Buratai ya jinjinawa musamman shi Mai martaba Omo N’Oba a kan kokarin da yake yi na ganin wanzuwar zaman lafiya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel