Gangamin masu laifi a Afrika ta yamma, Hukumar Yan sandan kasa da kasa tayi gargadi

Gangamin masu laifi a Afrika ta yamma, Hukumar Yan sandan kasa da kasa tayi gargadi

-Miyagun laifuka na addabar Afrika ta yamma ne saboda rashin wanzuwar isasshen bayani kan lamuran tsaron yankin

-An kulla yarjejeniya tsakanin hukumar yan sandan kasa da kasa da kuma kasashen Afrika ta yamma domin inganta tsaro a yankin

Sakataren Yan sandan kasa da kasa (Interpol) mai suna, Jurgen Stock yace masu aikata laifukan da suka shafi safarar miyagun kwayoyi, makamai da ma wasu abubuwa na daban na amfanin da rashin isasshen bayanai na sirri a tsakanin jami’an tsaron dake yankin Afrika ta yamma hakan ne yake basu damar cin karensu ba babbaka domin sun kasance suna gangami wajen aikata laifukan.

Stock ya fadi wadannan kalaman ne yayinda ake kulla wata yarjejeniya ta kaddamar da wani sashen da zai kula da samar da bayanai akan harkokin tsaron yan sandan Afrika ta yamma (WAPIS) da kuma hukumar ta yan sandan kasa da kasa ranar Talata, a birnin tarayya Abuja.

INTERPOL

INTERPOL
Source: Facebook

KU KARANTA:Mafarauta a Adamawa sun gudanar da zanga-zanga akan dan uwansu da ya rasu a hannun yan sanda

Ya kara da cewa sanya hannu akan wannan yarjejeniya, zai yi matukar taimakawa wajen fada da masu aikata miyagun laifuka a yankin. Yayinda yake jinjina ma kasashen Afrika ta yamma akan irin jajircewar da sukeyi akan samarwa yankin nasu tsaron da ya dace, Stock yace akwai bukatar hadin kai kwarai da gaske na kasashen domin cigaban wannan tsari da aka kaddamar na WAPIS wanda zai samar da bayanai akan harkokin tsaron kasashen Afrika ta yamma a kowace ranar mako.

Bugu da kari, “Bayanai kadan kawai muke dashi akan miyagun laifuka da kuma masu aikatasu a nan yankin Afrika ta yamma dama ita kanta hukumar yan sandan duniya. A don haka muke da yakinin cewa WAPIS zata samar da duk wani bayani da kan iya taimakawa wajen kawo wadannan laifuka kusa da yan sanda domin mangance matsalar ba tare da bata lokaci ba.

Shi kuwa Ministan tsaron cikin gida, Abdulrahman Dambazau cewa yayi, hakika gabatar da wannan tsari na WAPIS zai matukar taimakawa wajen kawo karshen miyagun laifunka dake addabar yankinmu da ma kuma masu aikata irin wadannan laifuka a yankin na Afrika ta yamma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel