Mutum 7 sun mutu, 58 sun jikkata a hatsarin mota a Kwara

Mutum 7 sun mutu, 58 sun jikkata a hatsarin mota a Kwara

- Hukumar da ke hana afkuwar hatsarurruka a hanya ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai a wani hatsari

- Hatsarin ya afku ne a gadar Osi a tsohuwar hanyar Ilorin-Jebba-Mokwa da ke karamar huumar Ilorin ta gabas da ke jihar Kwara

- Mutane 58 ne suka jikkata a hatsarin

Hukumar da ke hana afkuwar hatsarurruka a hanya a jiya Talata, 16 ga watan Afrilu ta tabbatar da mutuwar mutum bakwai a wani hatsari da ya afku a gadar Osi a tsohuwar hanyar Ilorin-Jebba-Mokwa da ke karamar huumar Ilorin ta gabas da ke jihar Kwara.

Wadanda abun ya shafa sun hada da maza uku da mata hudu; yayinda 34 daga cikin wadanda suka jikkata suka kasance manya mata 34 da kuma manya maza 24.

Mutum 7 sun mutu, 58 sun jikkata a hatsarin mota a Kwara

Mutum 7 sun mutu, 58 sun jikkata a hatsarin mota a Kwara
Source: Depositphotos

Daga cikin wadanda suka jikkata harda kananan yara 12.

Kwamandan FRSC, Uchechukwu Wihioka ya daura alhaki hatsrin, wanda ya wakana tsananin Toyota Dyna mai lamba 655 NAS da kuma Toyota Hiace mai lamba LSD919 SR akan shan gaba ba bisa ka’ida ba.

KU KRANTA KUMA: Sojoji sun yi ram da gungun masu garkuwa da mutane, sun ceto mutane 5 (Hotuna)

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Yan sanda a Zaria sun kama wasu yan fashi biyu da suka addabimasu mota a yankin Dumbin Rauga da ke hanyar babbar titin Zaria-Kaduna.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya tabbatar da kamun, inda yace an samo bindigar AK 47,alburusai da kuma layoyi daga yan fashin.

Da farko, wata majiya ta yan sanda a Zaria tace wasu tawagar yan sanda da suka tafi sintiri ne suka kama yan ta’addan bayan sun shige daji a lokain da suka hango motarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel