Buhari ya karbi bakuncin yan majalissar wakila Jam’iyyar APC

Buhari ya karbi bakuncin yan majalissar wakila Jam’iyyar APC

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin sabbun zababbun wakilai a karkashin dandamalin jam’iyar APC zuwa liyafa a fadar Shugaban kasar dake Abuja.

Liyafar ranar talatar itace ta biyu da shugaban ya taba shiryawa yan majalissar wakilan a wannan shekarar.

A watan Febrilu ya karbi bakunicnsu tare da sauran yan jam’iyyar akan tsarin mulki.

Liyafar ranar talatar ta gudana a tsakiyar shirin zaben yan majalissar wakilai da dattawa. Jigo a zaben sune kujerun shugaban majalissar wakilai da dattawa.

KU KARANTA: Wata amarya yar shekara 15 ta saka ma mijinta gubar bera a abinci

Shahararru a cikin jerin masu gwagwarmayan neman kujerar shugaban majalissar wakilai sune Shugaban masu rinjaye wato, Femi Gbajabiamila da Ahmed Wase mai wakiltar mazabar Wase a jihar Plateau.

Sauran sune Abdulrazak Namdas, wanda ke wakiltar Jada/Ganye, dake Jihar Adamawa; da kuma Ahmed Bago, mai wakiltar mazabar Chanchaga, a jihar Niger.

A bangare guda, Zawarcin kujerar shugaban majalisar dattawan Najeriya ya dau sabon salo yayinda wasu tsofin shugabannin majalisar dattawa biyu da tsohon kakakin majalisar wakilai daya suke bayyana goyon bayansu wa Sanat Ahmad Lawan.

Kana wasu tsofin gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suna goyon bayan Lawan.

Majiya ta bayyana cewa "Idan lokaci yayi, wadannan shugabanni zasu bayyana goyon bayansu a fili."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel