Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7

Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7

- An kama wasu 'yan sanda guda uku da suke da hannu wurin garkuwa da wata mata don karbar kudin fansa

- Kotu ta yankewa wadanda ake tuhumar hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Alkalin kotun ta yi fatan hakan ya zama darasi ga masu irin wannan dabi'ar ta satar mutane

A jiya ne wata kotu ta bayar da umarnin rataye wasu 'yan sanda guda uku tare da wasu mutane guda hudu da wata mata a cikinsu, wanda ta kama da laifin satar wata mata.

Kotun koli ta garin Uyo, cikin jihar Akwa Ibom, wadda mai shari'a Joy Unwana ke jagoranta, ta yankewa masu laifin hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7

Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7
Source: Depositphotos

Matar da aka kama tare da barayin sun, dauko ta haya ne ta dinga girkawa wadanda suka kamo abinci, akan za su dinga biyanta naira dubu hamsin.

Wadanda ake zargin sun hada da: Cpl Emmanuel Charlie, Ekaette Edet Moses, Fidelis Emmanson Jeremiah, Cpl Bassey Sunday (377812), PC Mfon Bassey (478463), Ndu Okon Johnny, Unyime Edem Etukakpan da kuma Itohowo Godwin Akpakwa.

KU KARANTA: El-Rufai ya kori ma'aikatan sa

Kotu na tuhumar su da laifuka guda uku, wanda suka hada da zalunci, garkuwa da mutane da kuma taimakawa wa barayin gabatar da satar ta su.

Mai shari'a Unwana ta ce: "Kotun ta yankewa wadanda ake tuhumar hukuncin kisa ne bisa dokar da jihar Akwa Ibom ta saka ta rataye duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane. Ina fatan hakan zai zama izina ga wadanda suke da shirin fara irin wannan ta'addanci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel