Atiku ya gabatarwa da kotu shaidar da yake da ita akan magudin zabe

Atiku ya gabatarwa da kotu shaidar da yake da ita akan magudin zabe

A karshe dai dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP ya gabatarwa da kotu kwararan shaidu da suke tabbatar da cewa shine ya lashe zaben shugaban kasa a zaben da aka gabatar ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata

Dan takarar shugaban kasa a babbar jam'iyyar adawa PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya jaddada kin amincewa da sakamakon zaben da hukumar zabe ta kasa ta bayar, inda ta ke nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya lashe zabe.

A lokacin da ya je ga kotun da ya kai karar, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bai wa kotun asu shaidu da ya samu a na'ura mai kwakwalwa da aka yi aiki da ita wurin zaben na shugaban kasa.

A sakamakon zaben da hukumar zabe ta kasa ta fitar ta nuna cewa a cikin jihohi 36 tare da babban birnin tarayya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kuri'u 15,191,847, inda Atiku Abubakar ya samu kuri'u 11,262,978.

Atiku ya gabatarwa da kotu shaidar da yake da ita akan magudin zabe

Atiku ya gabatarwa da kotu shaidar da yake da ita akan magudin zabe
Source: UGC

Amma a cikin shaidar da ya gabatarwa kotun, dan takarar shugaban kasar ya nuna cewa ya samu kuri'u 18,356,732, hakan ne ya bashi damar kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu kuri'u 16,741,430.

Sai dai kuma hukumar zabe ta kasa ta bayar da amsar cewa sakamakon zaben da Atiku ya gabatarwa kotu, an kirkire shi ne, saboda ba shi da tushe.

KU KARANTA: El-Rufai ya kori ma'aikatan sa

Amma kuma a amsar da suka mayarwa hukumar zaben ta kasa, Atiku da jam'iyyar PDP sun bayyana cewa, adireshin na'ura mai kwakwalwar da aka samo shaidar ya yi dai dai dana hukumar zabe ta kasa.

"Sai dai kuma mai magana da yawun shugaban kasa a harkar siyasa, Mista Festus Keyamo SAN, ya bayyana cewa idan ma adireshin ya zamo dai dai dana hukumar zabe, to tabbas anyi kutse ne cikin na'ura mai kwakwalwar aka saka."

Atiku da jam'iyyar PDP sun zargi shugaban hukumar zabe na kasa da aikata babban kuskure a ranar bayyana sakamakon zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel