Yan sanda sun kama yan fashin da suka addabi mutane a hanyar Zaria-Kaduna

Yan sanda sun kama yan fashin da suka addabi mutane a hanyar Zaria-Kaduna

Yan sanda a Zaria sun kama wasu yan fashi biyu da suka addabimasu mota a yankin Dumbin Rauga da ke hanyar babbar titin Zaria-Kaduna.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo, ya tabbatar da kamun, inda yace an samo bindigar AK 47,alburusai da kuma layoyi daga yan fashin.

Da farko, wata majiya ta yan sanda a Zaria tace wasu tawagar yan sanda da suka tafi sintiri ne suka kama yan ta’addan bayan sun shige daji a lokain da suka hango motarsu.

Yan sanda sun kama yan fashin da suka addabi mutane a hanyar Zaria-Kaduna

Yan sanda sun kama yan fashin da suka addabi mutane a hanyar Zaria-Kaduna
Source: Depositphotos

Majiyar ta kara da cewa: “Su biyar ne a motar, amma uku sun tsere. Mun gansu suna karkatar da motarsu zuwa daji daga babban hanya da misalin karfe 1 na tsakar dare kuma suna sanye da kayan sojoji.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama za ta kafa sansani a Nasarawa

“Hakan yasa muka zarge su, don haka muka yanke shawararbin samunsu zuwa dajin. Daya daga cikin yan fashin biyu da aka kama, Abdulhamid Tanimu, mazaunin yankin ne yayinda dayan, Muhammad Murtala, ya kasance dan Fulani wanda yazo daga Karu, Abuja kan gayyata. Har yanzu ana gudanar da bincike akan sauran mambobin tawagar.”

Daga bisani yan sandan sun kama abokan rakiyan yan fashin, ciki harda matar daya daga cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel