Rundunar sojin sama za ta kafa sansani a Nasarawa

Rundunar sojin sama za ta kafa sansani a Nasarawa

- Rundunar sojin saman Najeriya na shirin kafa sansaninta a filin jirgin sama na Lafia

- Tawaga daga hedkwatar rundunar sojin a Abuja sun ziyarci filin jirgin sama na Lafia sannan sun ga matakin da ci gaban da filin jirgin ke ciki

- Anyi nasarar bayar da filin ne a lokacin da Gwamna Umaru Al-Makura ya ziyarci hedkwatar rundunar sojin da ke Abuja sannan ya gana da sugaban hafsan sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar

Rundunar sojin saman Najeriya na shirin kafa sansaninta a filin jirgin sama na Lafia, babbar birnin jihar Nasarawa.

Wata tawaga daga hedkwatar rundunar sojin a Abuja sun ziyarci filin jirgin sama na Lafia sannan sun ga matakin da ci gaban da filin jirgin ke ciki domin gaggauta tsarin samun sansanin da kuma duba fili da gwamnatin jihar ta bayar kafa sansanin.

Tawagar sojoji na sama sun yi amfani da ziyarar wajen duba ayyukan da ke gudana a filin jirgin sama na Lafia da kuma yaba ma kokarin gwamnatin jihar Nasarawa wajen ganin ta cika bukatarsu.

Rundunar sojin sama za ta kafa sansani a Nasarawa

Rundunar sojin sama za ta kafa sansani a Nasarawa
Source: Facebook

Daga nan sai tawagar suka kai ziyarar ban girma ga mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Mista Silas Ali Agara, wanda yace, “Ina sake baku tabbacin jajircewar gwamnatin jihar wajen samar da waje mai dadin zama ga rundunari sojin sama domin ta gudanar da ayyukanta a sansaninta da ke filin jirgin sama na Lafia."

KU KARANTA KUMA: Majalisa ta 9: Babu dan PDP da zai shugabanci wani kwamiti a majalisar kasar – Oshiomhole

A tuna cewa anyi nasarar bayar da filin ne a lokacin da Gwamna Umaru Al-Makura ya ziyarci hedkwatar rundunar sojin da ke Abuja sannan ya gana da sugaban hafsan sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar, wanda ya nema wa rundunar fili don kafa sansani a Nasarawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel