Majalisar dokokin Jihar Ekiti ta dakatar da Segun Adewumi

Majalisar dokokin Jihar Ekiti ta dakatar da Segun Adewumi

Mun ji cewa Majalisar dokokin jihar Ekiti ta dakatar da daya daga cikin ‘Ya ‘yanta bayan ta same shi da laifin sabawa dokokin zaman majalisa. ‘Dan majalisar da aka dakatar shi ne Honarabul Segun Adewumi.

A Ranar Talata 16 ga Watan Afrilu ne majalisar jihar Ekiti ta yankewa Hon. Segun Adewumi, hukuncin dakatar da shi daga zaman majalisa na tsawon makonni 6 bisa laifin yin gardama da Kakakin majalisa a lokacin yana magana.

Laifin wannan ‘dan majalisa shi ne yin fito na fito da shugaban majalisar dokokin na jihar Ekiti watau Adeniran Alagbada, inda ya rika magana a lokacin shi ma yana yi. Wannan ya sa yanzu za ayi zaman makonni 6 ba tare da shi ba.

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar Jihar Benuwai yayi murabus kwatsam

Kakakin majalisar da yake jawabi jiya ya bayyana cewa yayi amfani da sashe na 17 na dokokin majalisar jihar inda ya dakatar da shi daga halartar wani zama da za ayi a zauren majalisar, amma ya kan iya yin wasu aikace-aikacen.

Rt. Hon. Adeniran Alagbada yake cewa muddin yana magana a matsayinsa na shugaban majalisa, babu wanda ya isa ya tsoma masa baki haka kurum don haka yake ganin Honarabul Segun Adewumi bai nemi zaman lafiya ba.

KU KARANTA: Ba mu goyon bayan Sanata Ndume inji Dattawan Borno

Adeniran yake cewa tsohon mataimakin Kakakin majalisar dokokin ya nuna cewa fito na fito yake yi da shi , don haka ya zama dole a hukunta sa. ‘Yan majalisar dokokin jihar kuma duk sun amince da wannan mataki da aka dauka a zaman.

Dakatar da ‘dan majalisar ke da wuya, sai wani Dakaren jami’in tsaro da ke aiki a majalisar ya tashi yayi waje da Segun Adewumi daga cikin zauren majalisar zuwa haraba domin cika aikin da Mai girma shugaban majalisar dokokin yayi.

Kamar yadda The Nation ta rahoto mana, ‘yan majalisar jihar sun yi ittifaki da wannan mataki da Kakakin ya dauka inda su ka nuna cewa shugaban majalisar bai karya wata doka ko yayi karfa-karfa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel