Dattawan Borno: Ba mu goyon bayan Ali Ndume

Dattawan Borno: Ba mu goyon bayan Ali Ndume

Kungiyar dattawan jihar Borno sun karyata rahoton da ke cewa suna marawa Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawa a matsayin shugaban kasar majalisa.

Kungiyar ta ce yin hakan zai kawo rabuwar kai tsakanin yan jihar Borno musamman dan majalisan wakilai, Betara Aliyu, da ke neman kujerar kakakin majalisar wakilar.

Sakataren kungiyar, Bulama Mali Gubio, ya ce ya zama wajibi suyi bayani ne bisa rahotannin da ke fitowa wanda ya jawo cece-kuce tsakanin mutanen jihar Borno.

KU KARANTA: Dakatar da Onnoghen na da nasaba da siyasa

Gubio yace: "Da farko, kungiyar dattawan Borno suna matukar ganin girman Sanata Mohammed Ali Ndume a matsayin dan jihar Borno.

"Amma, wannan kungiyar na fayyace rahotannin da ke cewa dattawan Borno suna goyon bayan Sanata Ali Ndume matsayin shugaban majalisar dattawa."

"Ku sani cewa a tarihin siyasarmu, jihar Borno da Yobe duk daya ne. An tsamo jihar Yobe ne daga Borno a shekarar 1991. Yawancin shugabannin jihar Yobe na da gidaje a Maiduguri."

"Duk da cewa 'ya'yan jihohin Borno da Yobe na da hakkin takarar siyasarsu amma mu a matsayin dattawan Borno da Yobe ba mu fitowa mu nuna goyon baya ga wani saboda duk abinda ya fito daga Yobe, yan Borno na farin ciki, kana duk abinda ya fito daga Borno, yan Yobe na alfahari.

"Bamu adawa da juna a fili. Wannan ya sabawa al'adarmu na matsayin dattawan Borno da Yobe. Sai da mu goyi bayansu duka ko muyi shiru."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel