Majalisa ta 9: Babu dan PDP da zai shugabanci wani kwamiti a majalisar kasar – Oshiomhole

Majalisa ta 9: Babu dan PDP da zai shugabanci wani kwamiti a majalisar kasar – Oshiomhole

- Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa babu wani dan jam’iyyar PDP da zai shugabanci wani kwamiti a majalisar dokokin kasar a wannan karon

- Oshiomhole ya bayyana haka ne a wani taron ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da zababbun ‘yan majalisar dokokin kasar na APC

- Yace ba za su ssake tafka kuskuren da suka yi a 2015 ba

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa babu wani dan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da zai shugabanci wani kwamiti a majalisar dokokin kasar a wannan karon.

Oshiomhole ya bayyana haka ne a wani taron ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi da zababbun ‘yan majalisar dokokin kasar na jam’iyyar APC a fadar Shugaban kasa a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.

Majalisa ta 9: Babu dan PDP da zai shugabanci wani kwamiti a majalisar kasar – Oshiomhole

Majalisa ta 9: Babu dan PDP da zai shugabanci wani kwamiti a majalisar kasar – Oshiomhole
Source: Depositphotos

Yace: “Mun yi kuskure a shekarar 2015 wajen zaben shugabanni, amma ba za mu sake irin wannan kuskure ba yanzu. Zababbun ‘yan jam’iyyarmu ne za su rike manyan mukamai a majalisa. Babu wani dan jam’iyyar adawa da zai rike kujerar shugabancin majalisa ko da ko guda daya ne.

KU KARANTA KUMA: Dattawan Borno: Ba mu goyon bayan Ali Ndume

”Da ‘yan Najeriya na son su da sun zabi PDP din. Kuma idan ba a manta ba a zamanin da suka sheke ayar su ai sune suke raba wa kansu kujerun shugbancin na kwamitin majalisa.

”Da dadaddun ‘yan majalisa da sabbi duk za a nada su shugabannin kwamitoci. Kowa zai samu mukami a majalisar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel