Shugaban masu rinjaye a Majalisar jihar Benuwai ya ajiye aiki

Shugaban masu rinjaye a Majalisar jihar Benuwai ya ajiye aiki

Mun samu labari cewa wani ‘dan majalisar dokoki a Najeriya yayi abin da ba a taba yi ba a jiharsa, inda ya rubuta takardar murabus daga aiki. Wannan abu dai ya faru ne a majalisar dokokin jihar Benuwai.

Honarabul Benjamin Adanyi wanda shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar dokoki na jihar ta Benuwai ya ajiye aikin na sa ne bayan dakatar da shi da aka majalisa tayi. Benjamin Adanyi ‘dan majalisa ne na APC kafin yanzu.

Benjamin Adanyi ya kasance yana wakiltar Makurdi ta Kudu a majalisar jihar Benuwai kafin Ranar Talatar da ta wuce, inda aka ji labarin cewa ya rubuta takarda tun Ranar 10 ga Watan Afrilun 2019 da nufin cewa ya ajiye aikinsa.

Adanyi ya kuma bayyana cewa dole ya ajiye aikin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sa a matsayin daya daga cikin Wakilan Arewa ta tsakiya a cikin hukumar NEDC da aka kafa domin farfado da Yankin Gabashin Arewa.

KU KARANTA: Babu mamaki Sanatoci da ‘Yan Majalisa su karkare aikin kasafin kudin 2019

Shugaban masu rinjaye a Majalisar jihar Benuwai ya ajiye aiki

Babban ‘Dan Majalisar Benuwai ya rubuta takardar ajiye aiki
Source: Twitter

Hon. Benjamin Adanyi ya bayyanawa majalisar cewa yayi nufin a ce ya sanar da ajiye aikin na sa a gaban majalisa yayin da ake zama, amma yace rikice-rikicen siyasa da majalisar ta samu kan-ta a ciki ne ya hana sa yin hakan.

‘Dan majalisar ya godewa ‘yan uwan sa a game da damar da su ka ba sa, har ya zama shugaban masu rinjaye. A 2018 ne aka dakatar da Adanyi da wasu ‘Yan majalisa 7 bayan sun yi yunkurin tsige gwamna Samuel Ortom na PDP.

Sauran ‘yan majalisar da aka dakatar tare da shugaban masu rinjayen majalisar sun hada da Honarabul Terkimbi Ikyange. Tun da aka kafa jihar Benuwai a 1976, ba a raba samun ‘dan majalisar da ya ajiye aikin sa ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel