An wuce wurin: APC ta dauki Gbajabiamila, ta mika kujerar mataimaki yankin arewa ta tsakiya

An wuce wurin: APC ta dauki Gbajabiamila, ta mika kujerar mataimaki yankin arewa ta tsakiya

Jam'iyyar APC mai mulki ta ce ta zabi Honarabul Femi Gbajabiamila a matsayin dan takarar shugaban majalisar wakilai da ta ke goyon baya.

Sakataren yada labaran jam'iyyar APC na kasa, Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan a wani takaitaccen bayani da ya fitar a dandalin sada zumunta (whatsapp) na jam'iyyar APC a ranar Talata. Ya ce zabin Gbajabiamila ya biyo bayan tattaunawar da mambobin jam'iyyar APC a zauren majalisar wakilai suka yi da shugaba Buhari yayin cin abincin dare tare a dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa.

Issa-Onilu ya bayyana cewar jam'iyyar APC ta mika kujerar mataimakin shugaban majalisar wakilai zuwa yankin arewa ta tsakiya.

Tuni dama jam'iyyar APC ta zabi Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takarar ta na kujerar shugaban majalisar majalisar dattijai.

An wuce wurin: APC ta dauki Gbajabiamila, ta mika kujerar mataimaki yankin arewa ta tsakiya

Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

Dangane da takarar ta Lawan, Legit.ng ta kawo muku labarin cewar jam'iyyar APC ta ce tayi maraba da yunkurin 'ya'yanta na neman goyon bayan mambobin jam'iyyar adawa a takarar neman shugabancin majalisa da suke yi.

A wani jawabi da ta fitar a ranar Lahadi, APC ta ce yin hakan ba laifi ba ne, a saboda haka bai ci karo da dokar jam'iyya ba.

DUBA WANNAN: A karon farko tun kafuwar Najeriya, an samu 'sa hannun' mace a kan takardar Naira

"Mun samu korafe-korafen cewar 'ya'yan jam'iyyar mu na gana wa da mambobin jam'iyyar adawa a kan siyasar cikin zauren majalisa. Muna son jama'a su san cewar jam'iyyar mu ba ta damuwa a kan irin wadannan gana wa ko tattauna wa. Siyasa, a ko ina cikin fadin duniya, ta gaji haka. Sannan mu na masu yin watsi da wasu rahotanni a kafafen yada labarai da ke bayyana cewar mambobin da suka yi hakan sun saba wa jam'iyya. Jam'iyyar APC ke da rinjaye a dukkan zauren majalisar kasa, a saboda mu na da yawan da zamu samar da shugabancin majalisa," kamar yadda ya ke a cikin jawabin da Lanre Issa-Onilu, sakataren yada labaran jam'iyyar APC, ya sanya wa hannu.

Jawabin na zuwa ne a matsayin martanin jam'iyyar APC a kan ganawar Sanata Ahmed Lawan, dan takarar shugabancin majalisa da fatar shugaban kasa ke goyon baya, da wasu mambobi da shugabannin jam'iyyar PDP. Za a yi zaben shugabannin majalisun tarayya a watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel