Rayuka 16 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa

Rayuka 16 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa

Cikin wani sabon rikici na makiyaya da manoma a Arewa ta Tsakiya, rayukan Mutane 16 sun salwanta tare da mutane 14 da suka jikkata yayin da 'yan bindiga suka bude wuta kan wata al'umma mahalarta bikin radin suna a ranar Talata.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, cikin wadanda suka riga mu gidan gaskiya yayin da azal ta afka masu a jihar ta Nasarawa sun hadar da jaririn da ake yi wa bikin radin suna, iyayen sa da kuma 'yan uwa da abokanan arziki mahalarta bikin.

Rayuka 16 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa

Rayuka 16 sun salwanta, Mutane 14 sun jikkata a harin jihar Nasarawa
Source: UGC

A yayin ci gaba da tsama ta rikicin makiyaya da manoma da ya ki ci ya ki cinyewa, hari ya auku ne a daren ranar Lahadin da ta gabata cikin kauyen Numa da ke karkashin karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mugun ji da mugun gani ya auku yayin 'yan uwa da abokanan arziki mahalarta bikin radin suna ba tare da aune ba suka ji saukar harsashi na bindigu da ya yi sanadiyar salwantar rayukan Mutane 16 tare da raunata mutane 14.

KARANTA KUMA: Mun datse 'yan Boko Haram a gabar tafkin Chadi da dajin Sambisa - Buratai

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda na jihar, Umar Shehu Nadada, yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar AFP, ya bayar da tabbacin aukuwar wannan ta'addanci kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel