Gasar zakarun turai: Messi ya yi gaba, Christiano ya koma gida

Gasar zakarun turai: Messi ya yi gaba, Christiano ya koma gida

Hasashen cewar za a hadu a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai (UCL) tsakanin Lionel Messi na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da takwaransa na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cgristiano Ronaldo, ba zai tabbata ba.

A yayin da kwallo biyu da Messi ya jefa a ragar kungiyar Manchester United ta taimaka wa kungiyar Barcelona zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, kwallo guda da Christiano ya saka a ragar kungiyar Ajax ba ta isa hayar da kungiyar Juventus zuwa mataki na gaba ba.

A wasa na biyu a zagaye na uku a cikin gasar UCL, kungiyar Barcelona ta samu nasara a kan Manchester United da ci 3 da 0. Kungiyar ta Barcelona ta saka jimillar kallo hudu a ragar Manchester United a wasanni biyu da suka fafata.

Yanzu dai ana saka ran kungiyar Barcelona za ta hadu da duk wanda ya yi nasa a tsakanin wasan da za a buga tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da takwararta ta FC Porto.

Gasar zakarun turai: Messi ya yi gaba, Christiano ya koma gida

Wasan Barcelona da Manchester United
Source: Getty Images

Sai dai, a yayin da Messi da kungiyar sa, Barcelona, suka samu damar ketare wannan zagayen, zuwa zagaye na gaba, wato na kusa da na karshe, Christiano da kungiyar sa, Juventus, sun sha mamaki a hannun kungiyar Ajax.

DUBA WANNAN: Mai rabo ka samu: Hukumar kwastam ta bude sahafin daukan manyan ma'aikata 3,200

Kungiyar Ajax ta kasar Neitherland ta lallasa Juventus, har gida, da ci 2 da 1. Wannan nasara ta bawa kungiyar Ajax tsallaka wa zuwa zagaye na gaba, na kusa da na karshe.

Ajax za ta hadu da duk wanda ya yi nasara a tsakanin kungiyar Tottenham da Manchester City, a wasan da za su buga a daren ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel