Wasu dalibai mata sun samar da wutar lantarki daga tarkacen bola

Wasu dalibai mata sun samar da wutar lantarki daga tarkacen bola

Wasu dalibai mata dake makarantar Mercy High School dake jihar Abia sun yi nasarar juyar da kashin dabbobi, na mutane da tarkacen gida zuwa wutar lantarki.

Shugabar makarantar, Lilian Chibiko,ta bayyana hakane a wani tattaunawa da tayi da NAN a kamar hukumar Umuahia dake jihar Abia.

Ta kara da cewa abinda ya rage kawai shine a juyar da iskar gas din zuwa tukunyar gas.

Chibiko tace tun lokacin da ta zama shugaba, malamanta da dalibanta sun horu akan kafuwa da samar da na’urar wuta daga hasken rana.

Legit.ng ta rahoto cewa shugabar tace "mun gwada kuma mun samu nasara abinda ya rage kawai mu juyar da iskar gas din zuwa silindoji kuma shine abinda muke bincike akai yanzu."

Bisa ga bayaninta ,tace tunda jami’ar Nigeria wato Nsukka(UNN) sun taba cin nasara akan hakan,makarantar ta zata ziyarce su dan karo basira .

Chiboki tace jajircewa akan binciken na’urar wuta mai amfani da hasken rana shine ya taimaka wurin samar da wutar lantarkin. “Yanzu muna da na’urar kuma muna kara bincike akan yadda zamu kawo dauki ga al’umma da shi."

Ta kara da cewa wasu daga cikin malamanta data horar suna fita domin kafa wannan na’urar kuma suna samin abin kashewa daga hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel