EFCC ta kama wani ‘Dan kasuwa da ya karbe Biliyoyi daga Bayin Allah

EFCC ta kama wani ‘Dan kasuwa da ya karbe Biliyoyi daga Bayin Allah

Jami’an hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa sun yi ram da wani ‘dan kasuwa mai suna Babagana Abba Dalori da ake zargi da laifin yin sama da fadi da kudin wasu.

Kamar yadda labari ya zo mana dazu, hukumar ta EFCC tayi ram ne da Babagana Abba Dalori mai shekaru 35 a Duniya da laifin karbar kudi daga hannun jama’a da niyyar cewa zai ba su makudan riba idan aka juya kudinsu.

Babagana Abba Dalori ya kan yi wa wadanda su ka kawo kudin su alkawarin cewa za su samu ribar kashi 135% ko ma kashi 200%. Wannan alkawari da zakin-bakin da ‘dan kasuwar yake yi, shi ne ke jawo masa tarin jama’a.

Wannan Bawan Allah ya bayyanawa EFCC cewa ya fara irin wannan sana’a ne a 2014, a lokacin yana amfani da Keke Napep wajen jigilar jama’a. Daga baya yace jama’a su ku nuna sha’awa a wajen harkar kasuwancin na sa.

KU KARANTA: An cafke wadanda ke satan kudin Bayin Allah ba su ji ba-ba su gani ba

Malam Abba Dalori yake fadawa EFCC cewa a 2014 ya samu tarin mutane da su ka shigo cikin harkar ta sa ana damawa da su, har ta kai ya shiga kasuwancin motocin haya da sauran hanyoyin samun kudi, ganin cewa harka ta bude.

Wanda ake zargin yace a 2016 ya bazama wajen harkar sufuri inda yake da motocin haya. Bayan nan ne kuma yace ya kashe kudi har Naira Miliyan 400 wajen samun lasisin hako ma’adani a cikin Abuja, har ya bude ofisoshi a jihohi 11.

KU KARANTA: Hukumar kwastam za ta dauki manyan ma'aikata 3,200

A 2017 ne jama’a su ka rika bulbolawa ko ta ina inda su ka rika zuba kudin su, wanda shi kuma ya tattara ya bude wuraren wankin mota da asibitoci da manyan otel da gidajen gona da dai sauran wuraren harkokin da za su kawo masa kudi.

Dalori ya bayyanawa jami’an EFCC cewa mutane kan kawo masa kudi daga Naira Miliyan 2 zuwa Miliyan 20 domin a juya masu. Daga karshe yace ya fara samun matsala ne bayan ambaliya ta rusa kadarorinsa har ta kai aka kama sa.

Abba Dalori kwararren Injiniyan wuta ne da yayi karatu a jami’ar tarayyar nan ta Maiduguri inda kawo yanzu yake kula da wani babban kamfani mai suna Galaxy Transportation & Construction Services LTD.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel