Mafarauta a Adamawa sun gudanar da zanga-zanga akan dan uwansu da ya rasu a hannun yan sanda

Mafarauta a Adamawa sun gudanar da zanga-zanga akan dan uwansu da ya rasu a hannun yan sanda

-Mafarauta sun gudanar da zanga-zanga akan dan uwansu da yan sanda suka kashe

-Hukumar yan sanda kuwa ta cigaba da bincike akan yanda hakikanin lamarin ya faru

Dimbin yan kungiyar mafarautan sun tare titin dake sadarwa zuwa ga shelkwatar yan sanda ta jihar Adamawa domin nuna bacin ransu akan dan uwansu da suke zargin yan sanda ne suka kashe shi.

Marigayin mai suna Ali Abdullahi,ya shiga hannun yan sandan ne bisa zargin da ake yi masa na satar mota inda yan sandan Doubeli suka yi gaba dashi zuwa tashar tasu.

Mutane da dama nada labarin cewa hakika an muzguna mashi wanda hakan yasa shi yayi doguwar suma kafin aka kai shi asibitin Kwararru ta Yola a ranar Litinin.

Gungun mafarauta

Gungun mafarauta
Source: UGC

KU KARANTA:JAMB ta damke mutane sama hamsin dake rubutawa wasu jarabawar UTME

Wata majiyar ta bayyana ma jaridar Daily Trust cewa a daidai lokacin da wannan mutum ya yanke jiki ya fadi a nan ofishin yan sandan, yan uwanshi sun nemi yan sandan su basu shi domin kai shi asibiti amma abin yaci tura har sai da ya kara kwana daya cikin wannan yanayin.

Mafarautan dai sun fito ne domin nuna fushinsu akan wannan lamari, wanda hakan kuwa ya sanya tuni aka dauki tsauraran matakan tsaro a daidai wannan yankin da zanga-zangar ke gudana.

Sakataren kungiyar mai suna Jibrilla Ahmad Modi wanda ya zanta da yan jarida jim kadan bayan da suka kammala wata ganawa da hukumar yan sanda yace tabbas an ci zarafin mamacin saboda an muzgana masa kwarai da gaske wanda shine ma dalilin da yayi sanadiyar rasa rayuwarsa akan zarginsa da ake na motar da bai sata ba.

Kafin a shawo kan wannan lamari sai da aka yi amfani da jami’an soji domin natsar da mafarautan.

Yayinda yake bada nashi jawabin, jami’in hulda da jama’a na yan sandan jihar mai suna Usman Abubakar ya shaidawa yan jarida cewa hukumar tasu na nan na bincike akan gaskiyar wannan lamari inda tuni ta tuge DPO na tashar yan sandan Doubeli su kuma wasu mutum hudu wadanda ke da hannu a cikin wannan lamarin aka tura su ofishin CID dake Yola domin gudanar da bincike akan su.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel